1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a aiyuakan jinkai a duniya

Al-Amin Suleiman Babayo/YBAugust 19, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware ranar sha tara ga watan Agusta domin tunawa da ma'aikatan jin kai, wadanda ke sadaukar da rayuwarsu don taimaka wa mutanen da ke bukatar agaji musamman ‘yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/1JlwV
Thema - Binnenflüchtline in Nigeria
Kungiyoyin agaji dai na kokari su kai wa 'yan gudun hijira tallafi duk da barazanar da su ke fiskantaHoto: DW/Uwaisu Idris

Bukin wannan shekarar dai na zuwa ne a dai dai lokacin 'yan gudun hijira a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya ke fama da yunwa inda karancin abinci mai gina jiki ke barazanar hallaka yara sama da dubu 500.


Najeriya dai na cikin kasashe da suka fi yawan ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidaje su wanda kuma ake zargin ana karkatar da kayan agaji da ake kai musu.


Akwai sama da mutane miliyan biyu wadanda suka tsere daga gidajensu sanadiyyar rikicin Boko Haram da ke da zama a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.


Akwai da dama daga cikin wadan nan ‘yan gudun hijirar da suka nemi a fitar da su daga cikin wannan kunci da suke ciki ko kuma mayar da su garuruwansu.

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Abinci na daga cikin manyan abubuwa da dan gudun hijira ke nema dan ya rayuHoto: Reuters/S.Ini


Alhaji Muhammad Bamai wani mazaunin Maiduguri ya yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta gaggauta tallafawa wadannan bayin Allah domin rage musu radadi da suke ciki bayan raba su da gidajensu da rikicin Boko Haram ya yi.


Ana alakanta halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki da yadda ake zargin karkatar da kayan abinci da aka nufa kai wa yankin kamar yadda Sanata Ali Ndume shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan kasar ya nunar.


Hukumomi dai na cewa na bakin kokarinsu wajen kyautata halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki. Sai dai ma'aikatan jinkai na fama da barazanar aiyukan wasu ‘yan bindiga wadanda kan kai hari kan ayarinsu.