1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Gaza

Zainab MohammedDecember 31, 2008

Jawabin Shugaban Palastinawa

https://p.dw.com/p/GQ2l

Shugaban Yankin Palastinawa Mahmoud Abbas yayi barazanar watsi da tattaunawar sulhu da kasar Izraela, a ɓangaren nuna adawarsa da irin ɓarnar da dakarun Izraela ke cigaba dayi a zirin Gaza.

Palästinenserpräsident Mahmoud Abbas
Mahmoud AbbasHoto: AP

A jawabin da yayi ta gidan talabijin da yammacin yau, shugaban yankin Palastinawan ya ce bazai ji nauyin watsi da tattaunawar ba, idan har suka cigaba da gasawa al'ummar mu aya a hannu.

Mahmoud Abbas dai yana mai mayar da martani ne dangane da kutse da hare haren yini biyar a jere da dakarun izraelan ke cigaba dayi a zirin Gaza.

Ya bayyana harin boma boman da kasancewa mugunta ta mummunar hanya,mara misaltuwa.

Mahmoud Abbas yace babu yadda zaa cimma warwarte rikicin ,idan har ba a bawa al'ummar Palastinawa yancin kansu ba. Yace ta yaya zaa cimma gano bakin zaren warware rikicin da kofarsa take a kulle?

Yace koda suna da niyyan cigaba da wannan tattaunawa na sulhu, da nufin ganin an cimma tudun dafawa, bisa dukkan alamu yanzu a bayyana take babu amfanin zama teburin sulhu da Izraela,idan akayi la'akari da halin da ake ciki.

To sai dai a ɓangarenta Izraela ta hakikance cewar wannan kutse da sukayi wa zirin Gazan na mai kasancewa martanin harin rokokin da aka harbawa a al'ummominsu ne daga yankin kamar yadda ministan tsaron Izraelan Ehud Barak ya sha jaddadawa...

Israel Verteidigungsminister Ehud Barak Regierungskrise
Ehud BarakHoto: AP

"Dakarun Izraela suna mayar da martani ne, da nufin kawo karshen ayyukan tarzoma, kuma zamu dauki mataki ta kowace hanya na tabbatar da hakan. A shirye muke na cigaba da kai waɗannan hare hare da faɗada kutsenmmu "

A yanzu haka dai titunan zirin Gaza tankar an share su ne da tsintsuya, bayan harin boma boman Izraelan na tsawon kwanaki biyar. Idan kaga mutane a waje, sun fito ne domin sayen burodi da sauran abunda za a kaiwa bakin salata.

An soke dukkan makarantu, an rufe shaguna, sai 'yan kalilan na sayar da ababai da suka danganci gasa buredi. Inda a wasu lokuta zakaga kimanin mutane 250 a layi suna jira domin saye.

Matsalar dai itace inji Palatinawan dake layin,bawai jiran layi yazo kanka ba, amma baka san ko zaka bar wurin da ranka ko kuma cikin koshin lafiya ba, saboda barazanar harin boma boman Izraela da jiragen yaki.

Izraelan dai tayi watsi da kiraye kiraye da kasahen duniya keyi mata na dakatar da wannan hari data kaddamar akan yankin Palastinawan.

Benjamin Natanyawu na jami'iyyar Likud mai adawa a Izraela yace wannan rikicin bamai karewa bane a yanzu..

Benjamin Netanyahu
Benjamin NetanyahuHoto: AP

"Yace kawunanmu a hade suke, babu batun adawa ko kuma hadaka a a wannan yunkuri namu na dakatar da barazanar da akeyiwa branemmu, kuma zamu dauki kowane mataki na cimma bukatummu"

Kawo yanzu dai palastinawa kusan 400 suka rasa rayukansu, bayan sama da dubu ɗaya da suka jikkata. Duk dacewar Primiyan Izraela Ehud Olmert ya hakikance cewar suna daukar matakai na ganin cewar harin bai taɓa fararen hula ba, rahotanni daga Zirin Gazan na nuni dacewar daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwa mata da yara kanana kusan 100.