1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Iraƙi na da sarƙaƙƙiya da takaici

September 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuBm

Babban kwamandan dakarun Amirka a Iraqi Janar David Petraeus ya fadawa majalisar dokokin Amirka cewa karin sojin da aka yi a Iraqi wata nasara ce kuma ana cimma manufofin daukar wannan mataki na soji. To amma Pertraeus ya yi kashedin cewa janye sojojin ba tare da an yi wani kwakwaran shiri ba, ka iya zama wani babban bala´i. Duk da haka dai ya ce ana iya janye sojojin Amirka kimanin dubu 30 kafin watan yulin shekara ta 2008 sannan rukunin farko na sojojin ka iya barin Iraqi a cikin makonni kaliklan masu zuwa.

Petraeus:

Ya ce “Duk da wannan ci-gaba da ake samu har yanzu halin da ake ciki a Iraqi mai sarkakiya ne kuma wani lokaci yana da takaici. Amma na yi imani zamu cimma manufofinmu a Iraqi amma hakan ba zai zo cikin sauri ko cikin sauki ba.”

Shi ma jakadan Amirka a Bagadaza, Ryan Crocker ya ba da bahasi akan halin da ake ciki a Iraqi inda ya ce ana samun ci-gaba duk da cewa gwamnati ba ta samun cikakken goyon baya na siyasa.