1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Irak

December 8, 2005
https://p.dw.com/p/BvHQ

Kungiyyar masu tsattsauran raáyi a Iraki, tace ta dage lokacin data shirya kisan masu yada Addinin Kiristan nan guda hudu da suke garkuwa dasu, har zuwa kwana biyu a nan gaba.

Ya zuwa yanzu dai babu wani dalili da kungiyyar ta bayar na daukar wannan sabon mataki.

A waja daya kuma, tsohon shugaban kasar Jamus , wato Gerhard Schröder ya bayyana a gidan talabijin din Aljaeera, yana daukaka kira ga wadanda suka yi garkuwa da Bajamushiyar nan a irak, da suyiwa Allah su yiwa annabi su sako ta.

Shugaba Schröder yaci gaba da cewa, bajamushiyar mai suna Susanne Osthoff tuni ta musulunta tare da zabar kasar Iraqi a matsayin kasar da zata zauna .

Idan dai za a iya tunawa, makonni biyu da suka gabata ne akayi garkuwa da Sussanne Osthoff a kasar ta Iraqi.

A wata sabuwa kuma, jami´an yan sanda a kasar ta Iraki sun shaidar da tashin wani bom a cikin wata mota kirar Bus a birnin Bagadaza, wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwar Mutane 30 tare da jikkata wasu 25.