1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Iraki

Zainab A MohammadMay 18, 2005

Ziyarar ministan harkokin wajen Iran Kamal Kharazi a Iraki

https://p.dw.com/p/Bvbs
Hoto: AP

Gwamnatin Iran dana Iraki sun lashi takobin inganta harkokin tsaro aciki da kewayen Iraki,a wani abun da ke zama juyawa gabar dake tsakanin kasashen biyu baya.

Wannan furucin yazo ne adaidai lokacin da ake cigaba da kai kazaman hare hare hare sassa daban daban a Irakin.Da safiyar yau ne dai yan bindiga dadi suka harbe Brigadier general ibrahim Hamas dake maaikatar cikin gida a wannan kasa,adaidai lokacin dayake barin gidansa zuwa wurin aiki.Bugu da kari mai dakinsa ta samu raunuka ayayin wannan harin da yayi sanadiyyar ran maigidanta.

A yau ne dai ministan harkokin wajen Iran ya shiga yini na biyu a wannan ziyara dayake a iraki,wanda ke zama karo na farkon irinsda tun bayan kifar da gwamnatin Sadam Hussein.

Tun a jiya ne ministan harkokin wajen Iraki Hoshyar Zebari yace ko shakka babu wannan ziyara ta Kamal kharazi zata taimaka matuka gaya wajen dinke barakar dake tsakaninsu tare da inganta dangantaka ta kut da kut.Yace gwamnatin Iraki na yanzu mai nema zaman lafiyace musamman da makwabtanta,sabanin zamanin mulkin Sadam.

Khamal Karazi ya tabbatarwa takwaransa na Iraki cewa gwamnatin darikar Shia ta Iran bazata tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Irakin ba.Sai dai bada goyon bayanta wa samara da zaman lafiya.Ministan na Iran yace a matsayinsu na makwabtan Iraki,basa muradin cigaba da ganin halin kakanikayi da Iraki ke cigaba da kasancewa ciki ta fanning tsaro.

Wannan ziyara ta Kharazi wadda tazo yini biyu bayan ziyarar sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice,na mai tabbatar ingancin dangantaka tsakanin makwabtan biyu,wadanda suka gwabza yaki daga shekarata 1980-1988.

A sauran sassanan Irakin kuma an wayi gari cikin hare haren yan yakin sunkuru wanda dakarun Amurka suka danganta da magoya bayan Abu Musab al-Zarqawi.

A yan makonni da suka gabata dai sama da mutane 500 suka rasa rayukansu akasarinsu kuwa fararen hula daga irin wadannan hare hare na yan yakin sunkuru.

A dangane da wadannan tashe tashen hankula ne ministan tsaro na Iraki ya lashi takobin tsananta matakan tsaro.Ayau din dai mutane 11 suka rasa rayukansu a hare haren boma bomai.sabon ministan tsaron da aka nada daga darikar Sunni Saadun al-Dulaimi yace zasu tabbatar dacewa Iraki ta kasance aljannar duniya wa mazauna cikin ta.