1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A IRAKI.

Zainab MohammedSeptember 30, 2004

Sama da mutane 35 suka rasa rayukansu a harin boma bomai a kudancin Bagadaza.

https://p.dw.com/p/Bvg5
Harin boma bomai.
Harin boma bomai.Hoto: AP

An wayi gari cikin hare hare a sassa daban daban na kasar Iraki Ayau,wadanda sukayi sanadiyyar rayukan yan kasar masu yawan gaske.

Akalla mutane 35 suka rasa rayukansu ,sakamakon tashin wasu boma bomai daga cikin motoci guda 3 a kusa da inda ayarin sojin Amurka ke wucewa,ayayinda sama da mutane 120 akasarinsu yara kanana suka samu raunuka,ata bakin likitoci da majiyan asibiti,a kudancin birnin Bagadaza.Wannan harin boma bomai yazo saoi kalilan bayan wani dan kunar bakin wake ya tayar da bomb dake jikinsa,wanda yayi sanadiyyar mutuwan yansandan Irakin biyu da sojin Amurka guda,acikin motarsa a wurin binciken motocin sojin Amurka dake yammacin fadar Irakin.

A yanzu haka dai ana cigaba da fuskantar tashe tashen hankula a Iraki,ga rashin tabbas ,makonni kalilan gabannin zaben shugaban kasa a Amurka ,a hannu guda kuma watanni 4 kafin zaben kasa baki daya a Irakin.Ayanzu haka dai hare haren da ake afkawa Sojin Amurkan dashi a tashi daga 40 zuwa 80,a kowane wata.A hare hare haren na yau babu tabbacin adadin fararen hula da suka rigamu gidan gaskiya.Hukumomin asibitin Yarmouk,inda akayi harin sun sanar da karban gawawwakin mutane akalla 35 ,banda wasu 120 da suka jikkata.Mazauna garin sun bayyana cewa ,ana bukin dashen itatuwa na wannan shekara ne,lokacin da aka afka da wannan harin.

A wani harin na daban kuwa wani sojin amurka ya bakunci lahira,sakamakon harin rokoki wa sansaninsu dake Bagadaza,baya ga harin daya kashe wani sojin Amurka guda,da yansandan Irakin biyu,harin daya raunana mutane 60,mafi yawansu mata da yara kanana.

Acan garin Falluja dake hannu yan tawaye kuwa,mai tazarar km 50 yammacin Bagadaza,Dakarun Amuerka sun rusa wani gini da sukace mayakan Abu Musab al-Zarqawi na fake aciki,kungiyar dake barazanar cewa zata fille kakannan Britanian nan da ake cigaba dayin garkuwa dashi.

A kusan kowane wayewan gari dai ana fuskantar kazamin hare hare a Falluja,inda Amurkawan ke kokarin murkushe yan yakin sari ka noken wannan yankin,wadanda suke zargi da hare haren da ake afkawa yan kasashen waje dasu,da harin boma bomai,musamman na kunar bakin wake.

Sai dai acigaba da sace sacen baki da akeyi a wannan kasa,wata kungiyar masu tsattsauran raayi na addinin Islamata sanarda yin garkuwa da mutane 10,wadanda suka hadar da mata yan kasar Indonesia guda 2,da yan Lebanon 2,kamar yadda gidan talabijin dinAljazeera ta yayataAn dai gabatar da mutane 4 daga cikin wadanda aka sacen,da bakin bindiga a kawunansu,daga baya ne aka nuna matan biyu daure da mayafi a kawunansu.To sai dai Aljazeera bata bayyana bukatun wadannada suka sace mutane goman ba.A baya dai irin wadannan kungiyoyin sun bukaci yan kasashen dasu fice daga Irakin ,idan har suna muradin a sakar musu wadanda ake garkuwa dasu.

Wannan kungiyar dai na mai zama reshen kungiyar Islamin Army in Iraq,wadanda ke tsare da yan jaridan Faransa tun daga ranar 20 ga watan Augustan daya gabata.Da farko dai kungiyar ta bukaci gwamnatin faransan daga janye dokar nan data kafa na haramta daurin Dankwali a makarantun gwamnati.Ayayinda ake wannan,gwamnatin rikon kwaryan Irakin ta sake tabbatar dacewa zata samar da zaman lafiya da tsaro a garin Falluja,nan da watan Nuwamba,kuma babu gudu ba ja da baya dangane da zaben kasar dazai gudana a watan janairun shekarata 2005,idan Allah ya kaimu.