1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A IRAKI

ZAINAB AM ABUBAKAR.November 10, 2003
https://p.dw.com/p/Bvni
Majalisar mulki a Iraki na ganin cewa zata iya cimma waadin da aka kayyade mata,duk da karuwan tashin hankali a wannan kasa.Daya daga cikin wakilan majalisar ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa zasu cimma waadin da aka debar musu na 15 ga watan Disamba. A jiya ne Kantoma Paul Bremer yaya gargadi wa wakilan majalisar 24 kann su tabbatar da cikanta wannan waadi da aka kebe musu.
Kudurin komitin sulhu na MDD 1511 a watan daya gabata yayi kira ga majalisar Irakin datatsara kundun tsarin mulki tare da gudanar da zaben kasa ranar 15 ga watan Disamba.
A dangane da hakane Bremer a ranar 6 ga wannan wata ya gana da wakilai 9 dake kewayen shugabancin majalisar dasu tabbatar da wannan rana da aka kayyade musu.A nasu bangare yan majalisar na cigaba da danganta kowane jinkiri ake samu da harkoki na hare hare da ake cigaba da kaiwa dakarun taron dangin dake cigaba da kasancewa a wannan kasa.Kana ga rashin basu dama a bangaren wakilan Amurka dake Bremer kewa jagoranci.
Majalisar dai na bukatar a bawa Iraki madafan iko kann harkokin tsaro tare da sukan yadda ake bada kwangilan sake ginin kasar wa masanaantun waje.
A dangane da hakane suka bukaci kasancewa cikakkun masu gudanar da mulki na Iraki amma ba masu taimakawa a lokacin da ake bukata ba. Shi kuwa ministan harkokin wajen Iraki Hoshyar Zebari ,cewa yayi rashin tabbatar da tsarin majalisar na kawo cikin wajen yanke kowane irin hukunci kann batutuwa da suka shafi kasar.
A halin da ake ciki yanzu haka Amurka ta rasa dakarunta kimanin 151 tunda ta sanar da mamaye a wannan kasa,ta dauki daidai da akewa dakarun na Amurka.A jiya hadarin harbin roka ya ritsa da wani sojin na Amurka a kudancin bagadaza.Irin harin da Amurka ke cigaba da zargin yan kungiyar Alqaeda da aikatawa da magoya bayan tsohon shugaba Sadam Hussein.
Paul Bremer a na shi bangare yace babu gudu babu ja adabaya acigaba da kasancewan sojojin taron dangin a wannan kasa,domin ficewa zai kasance babban asara ne garesu.