1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI KANN RATTABA HANNU BISA KUNDIN TSARIN MULKIN KASAR DA AKA SHIRYA YI YAU JUMA;A.

March 5, 2004

WAN NAN HOTON MR ADNAN PACHACHI NE DASHI DA WASU MAMBOBI NA GWAMNATIN RIKON KWARYA NA IRAQI KEWA MANEMA LABARAI BAYANI.

https://p.dw.com/p/BvlU
Hoto: AP

A yayin da gwamnatin Rikon kwarya ta iraqi da kuma mdd ke dakon zuwan wannan rana ta Juma,a don rattaba hannun amincewa da kundin tsarin mulkin kasar sai gashi a karshen taron rattaba hannun na yau mambobin darikar shi,awa ta kasar sun hau kujerar nakin yxarda da kundin tsarin mulkin bisa wasu dalilai.

A dai ranar litinin din data gabata ne gwamnatin rikon kwaryar ta amince da kundin da gagarumin rinjaye,amma kuma shugaban Shi,awan Ali al Hussain Al sistani yaki amincewa da,a rattaba hannun amincewa a maimakon mabiya darikar ta shi,a dake kasar.

Babban dai dalilin rashin amincewar daga bangaren yan shai,ar shine batun daya yi magana kann yadda za,a kafa gwamnatin dimokradiyyar kasar ta nan gaba.

A misali a cewar daya daga cikin shi,awan kundin tsarin mulkin da gwamnatin rikon kwaryar ta tsara ba zai basu damar yin kakagida a da yawa daga cikin mukaman kasar ba,a don haka sukace ba zasu yarda da kundin tsarin mulkin ba.

Hamed Al bayati daya daga cikin mai baiwa jamiyyar shi,awan shawara cewa yayi akwai babbar alamar tambaya kann kundin tsarin mulkin,domin kuwa babu yadda zaayi ace za,a daidaita kabilar da bata da magoya baya da yawa da kuma kabilar da take da al,umma da yawa. A don haka a cewar sa akwai sake.

Bisa wan nan rashin fahimtar juna da aka samu kuwa,mambobin gwamnatin rikon kwaryan sun gudanar da taron gaggawa don shawo kann al,amarin amma abu yaci tura.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa yarda da wan nan kundin tsarin mulki daga yan kasar shine tubali da zai bawa kasar Amurka dawowa da yan kasar mulkin su a hannun su ta hanyar gudanar da zabe a karshen watan yuni na wan nan shekara da muke ciki kamar yadda aka tsara.

A waje daya kuma daya daga cikin mambobin gwamnatin rikon kwaryar ta iraqi daya fito daga kabilar kurdawa,Mahmud Othman ya shaidar da cewa magoya bayan darikar shi,ar a baya sun kawo tsaiko har sau biyu dangane da wan nan shiri na mayar da mulki da Amurka ta tsara ga yan kasar ta iraqi,kana a yanzu kuma gashi ta kawo tsaiko na uku.

Mahmud Othman yaci gaba da cewa bai kamata ace wadanda basu da rinjaye a kasa na son tursasawa masu rinjaye ba. A takaice dai hannun ka mai sanda yake ga yan darikar ta Shi,a.

A lokacin gudanar da wan nan taro na yau rahotanni sun shaidar da cewa yan makaranta sun halarci gun da yawan gaske a hannu daya kuma da wasu daga cikin al,ummar kasar don ganewa idon su yadda bikin rattaba hannun zai kasance.

A yanzu haka dai babu wanda ya san lokacin da za,a sa hannun amincewa da wan nan kundin tsarin mulki,a hannu daya kuma da yadda yanayin mikawa yan kasar mulki zai kasance a nan gaba.

A baya dai an sa ran a larabar data gabata ne za,a sa hannun sai kuma aga daga sakamakon wasu tahwayen hare hare biyu da aka kai birnin Bagaza da karbala,wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 200 ban da da dama da suka jikkata.

Duk kuwa da matakan tsaron da aka dauka a gurin sai da wasu tsageru yan fadan sari ka noke suka harba wasu gurneti wasu tituna na birnin Bagadaza.

A hannu daya kuma tsagerun suka harba wasu gurnetin izuwa filin saukar jirgin saman kasar,to amma rahotanni sun shaidar da cewa babu wanda ya samu rauni.