1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Iraqi yau

Ibrahim SaniMay 17, 2006

Anm dage sauraron shari´ar da akewa Saddam Hussain da mukarraban sa izuwa mako mai zuwa

https://p.dw.com/p/BvTb
birnin Bagadaza
birnin BagadazaHoto: DW

Ya zuwa yanzu dai babban abin da yafi daukar hankali a zaman kotun na yau shine, na yarda da Alkalin kotun yayi na kyale Saddam Hussain da kuma Barzan Ibrahim, bada shaida a game da tuhumar take hakkokin bil adama da ake zargin Taha yassin Ramadan ya aikata a lokacin zamanin mulkin na Saddam.

Da farko dai masu gabatar da kara sun shaidar da cewa a lokacin da dakarun soji bisa umarnin Saddam Hussain suka kutsa garin Dujail a shnekara ta 1982, Taha Yassin Ramadan na daya daga cikin jami´an gwamnati da suke bawa dakarun Sojin Umarni,to amma a hannu daya Taha Yassin Ramadan ya karyata da cewa bashi a cikin garin a lokacin da al´amarin ya auku.

A cewar Taha Yassin Ramadan, wanda na daya daga cikin mukarraban Saddam Hussain da ake zargi da aikata miyagun laifuffuka a lokacin zamanin mulkin na Saddam, Ya tabbatar da cewa bashi da wani da zai bayar da shaida a game da abin da ya fadi Illa, Saddam Hussain da kuma tsohon Jami´in leken asiri na kasar wato Barzan Ibrahim al Tikirit.

Bayan daukar matakin kin amincewa da bukatar da Taha Yassin Ramadan yayi, daga baya kuma sai Alkalin Kotun ya amsa wannan bukata, duk da cewa ya zuwa yanzu ba a tantance lokacin da Saddam Hussain da Barzan Ibrahim Al Tikirit din zasu amsa tambayoyin da za´a yi musu ba a game da wannan batu da Taha Yassin Ramadan din ya gabatar ba.

Rahotanni dai daga Birnin Bagadaza, inda ake gudanar da taron sun shaidar da cewa an dage sauraron shari´ar izuwa ranar litinin mai zuwa bayan an saurari shaidu masu kare wadanda ake zargi a kalla guda tara.

A kuwa yayin da aka dage sauraron shari´ar ta Saddan da mukarraban nasa bakwai, a waje daya kuma rahotanni sun nunar da cewa majalisar dokokin kasar ce ta gudanar da wani taro na bayan fage.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewa kusan dukkannin bangarorin dake rikici da juna sun samu halartar wannan taro, a kokarin da suke na ganin an kafa gwamnatin hadaka da zata sami wakilcin dukkkannin jam´iyyun dake kasar.

Ya zuwa yanzu dai kafafen yada labarai sun rawaito wani jami´in diplomasiyya na Amurka na fadin cewa da alama kafa gwamnatin hadakar ta Iraqi ka iya daukar dogon lokaci, sabanin hasashen da akeyi cewa komai zai kammala nan bada dadewa ba.

Idai dai za a iya tunawa, a lokacin da kasar ta Iraqi ke cikin rudani na siyasa a dai dai lokacin ne kuma kasar take ci gaba da fuskantar tashe tashen hankula da kuma rikice rikice.

A misali ko da a jiya sai da mutane 50 suka ce ga garin ku nan wasu kuma da dama suka jikkata, a sakamakon tashin bama bamai a fadin kasar ta Iraqi baki daya.