1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Iraqi

Hauwa Abubakar AjejeDecember 20, 2005

Gamaiyar kungiyoyin yan sunni a kasar Iraqi ta koka da sakamakon farko farko na zaben yan majalisa da aka fito da shi,tana mai yin kira ga hukumar zabe data sake kirga kuriun.

https://p.dw.com/p/Bu3E
Hoto: AP

Taraiyar jamiyun yan sunni 3 da tayi takara a zaben yan majalisar dokokin karo na farko,ta fito ta yi Allah wadai da abinda ta kira,magudin zabe da kuma karya dokokin zabe,a lokacin zaben nay an majalisa.

Daya daga cikin shugabannin gamaiyar jamiyun ta yan sunni,Adnan al-Dulaimi ya baiyanawa manema labarai shakkunsu game da sakamakon farko da hukumar zabe ta fito da shi,wanda ya baiwa yan shia rinjaye.

Sakamakon bayan fage da hukumar ta bayar ya nuna cewa,jamiyar yan shia tana da kashi 58 cikin dari na kuriun da aka kada a birnin Bagadaza,yayinda kuma gamaiyar jamiyun sunni ta samu kashi 18.6 cikin dari na kuriun na Bagadaza.

Su dai shugabannin sunni sun bukaci hukumar zabe da ta sake duba sakamom zaben tare da nufin yiwa sakamakon da aka rigaya a sanar a yanzu gyara.

Wani memba na jamiyar Iraqi Islamic Party,daya daga cikin jamiyun sunni,Tareq al Hashim,yace,har yanzu akwai sauran lokaci da hukumar zabe ta Iraqi zata sake duba sakamakon zaben,idan ba haka ba kuwa inji shi,itace zata dauki alhakin dukkan magudi da aka yi a zaben,wanda kuma zai janyo mummunar illa ga tsaro da tattalin arzikin kasar.

Haka shima,sakatare janar na jamiyar yan gurguzu,Hamid Majid Musa,ya baiyana nashi damuwa game da wannan zabe,inda ya kira sanarda sakamaon zaben da hukumar zaben tayi rashin sanin ya kamata.

Wadanan zarge zarge dai sun zone a lokacinda shugaba Bush na Amurka,yake neman yan Iraqin su gagguta kafa gwamnati ba tare da bata lokaci ba.

Shima dai shugaban kasar Iraqin,Jalal Talabani,ya roki da a kafa gwamnatin gamin gambiza da zata hade dukkan kabilu da jamiyun siyasar kasar.

Yace yana son gwamnatin da zata hade kowa da kowa,larabawa,Turkawa da Kurdawa,yace,ba zai yiwu mafiya rinjaye suyi mulkin Iraqi tare da yin watsi da yan tsiraru ba.

Talabani,wanda yace ba zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa ba,yayi watsi da kararrakin zabe fiye da 200 da aka shigar,yana mai cewa wasu daga cikinsu basu da tushe.

A halin yanzu dai hukumar zabe ta kasar tayi watsi da kira da gamaiyar kungiyoyin yan sunni tayi mata na sake kirga kuriun da aka jefa a Bagadaza.

Hukumar tace,ya zuwa yanzu dai babu wani dalili da zai sanya a sake kidaya kuriun,yana mai baiyana bukatar yin hakan da yan sunni sukayi da cewa hali ne na siyasa kuma suna da ikon yin hakan.

A halin da ake ciki yau din a Iraqin an samu kaiwa hare hare a kasar ta Iraqi,bayan dan kwanciyar hankali da aka samu lokacin zabe.

A safiyar yau din nan aka sace direban jakadan kasar Jordan a Iraqin,kwana daya bayan wata kungiyar masu gwagwarmaya ta fito da hoto a internet cewa ta kashe wani dan kwamgila na Amurka,hakazalika wasu yan Iraqin 6 sun rasa rayukansu a yau din nan wasu yan sanda 3 kuma an harbe su har lahira a garin Tuz,arewacin Bagadaza,wasu yan Iraqin 2 kuma da suke aiki a wani sansanin sojin Amurka sun halaka a garin Balad.