1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Iraqi

Ibrahim SaniFebruary 27, 2006

Batun zaman lafiya a iraqi har yanzu yana kasa yana dabo

https://p.dw.com/p/BvTk
Mutadar Sadr
Mutadar SadrHoto: AP

Ya zuwa yanzu dai duk da kiraye kirayen da shugabanni na siyasa da addinai daga bangarori daban daban suka yi a kasar ta iraqi a makon daya gabata game da zaman lafiya , a iya cewa har yanzu ba a rabu da bukar ba.

Bukatar neman zaman lafiyar dai tazo ne, bayan da aka kai wasu hare hare ga muhimman ibadar mabiya darikar shi´a, a kasar ta Iraqi a makon daya gabata, wanda hakan ya harzuka wasu daga cikin su na lailai sai sun dauki fansa.

A cewar rahotanni dai mutane a kalla 25 ne suka rasa rayukan su a jiya lahadi sakamakon tashe tashen hankulan da aka fuskanta.

Bugu da kari bayanan sun kuma tabbatar da cewa wani hari da aka kai da gurneti a Bagadaza, ya haifar da rasuwar wasu mutanen 16 kana a daya hannu kuma bom daya tashi a yankin Hilla da yayi kaurin suna wajen fuskantar tashe tashen hankula a kasar ta iraqi ya haifar da mutuwar mutane biyar.

Daga dai tun lokacin da aka kai wannan hari izuwa guraren ibadar ta mabiya shi´a n a makon daya gabata, ma´aikatar tsaron kasar ta Iraqi ta tabbatar da cewa mutane 120 ne suka rasa rayukan su a sakamakon tashe tashen hankula da rikice rikice da suka wakana.

To amma kuma a wata majiya ta daban, an tabbatar da cewa yawan mutanen da suka rasa rayukan nasu yafi wan nan jumla da aka bayar a hukumance.

Bisa kuwa irin wannan hali da ake ciki a kasar ta Iraqi na rashin tabbataccen tsaro da kuma zaman dar dar, ya haifar, daya daga cikin shugabannin na yan shi´a wato Muqtadar Sadr yin kira ga magoya bayan sa nasu kwantar da hankalin su don samun hadin kai a tsakain al´ummar kasar ta Iraqi.

Don ganin cewa an samu biyan bukata game da hakan, Muqtadar Sadr ya bukaci mabiya darikar sunni a kasar dasu gudanar da addu´oi na zaman lafiya tare da yan shi´a a ranar juma´a mai zuwa Idan Allah ya kaimu.

Rahotanni dai daga kasar ta Iraqi sun shaidar da cewa an cire dokar ta bacin hana abubuwan sufuri zirga zirga a yau litinin din nan a Birnin Bagadaza, to amma batun dokar hana yawon dare da aka saka na nan daram.

A waje daya kuma, bayanai sun nunar da cewa tsohon shugaban kasar ta Iraqi wato Saddam Hussain ya kawo karshen yajin aiki da yake na kin cin abin ci daya fara a watan daya gabata.

Saddam Hussain ya dauki wannan matakin ne don nuna bacin sanda a game da yadda ake gudanar da shari´ar sa daya kira babu adalci da gaskiya a cikin ta.

Rahotanni dai sun nunar da cewa Saddam Hussain wanda ya shafe kwanaki 11 yana yajin kin cin abincin ,ya koma cin abin cin ne a bisa dalili dake da nasaba da rashin lafiya.

A wani sabon labarin kuma, a gobe talata ne ake sa ran Faraministan kasar ta Iraqi wato Ibrahim Al Jafari zai kai ziyara izuwa kasar Turkiyya. Bayan kammala ziyarar tasa ana sa ran Mutadar Sadr kuma ya kai tasa ziyarar izuwa kasar ta Turkiyya.