1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

June 25, 2004

DAKARUN SOJIN AMURKA A IRAQI.

https://p.dw.com/p/Bvif
Hoto: dpa

Sakamakon tashe tashen bama bamai da aka fuskanta a garuruwa hudu a iraqi a jere daya bayan daya jiya alhamis a iraqi a yau juma a dakarun sojin hadin gwiwa sun kara daurara matakan tsaro a gurare daban daban na kasar musanmamma Birnin Bagadaza.

Rahotanni sun nunar da cewa dakarun sojin sun dauki wan nan matakin ne sakamakon kwanaki dake kara karatowa na mika mulki hannun yan kasar ta Iraqi daga hannun dakarun sojin mamaye da Amurka kewa jagoranci.

Bugu da kari akwai kuma hasashen cewa kungiyoyin da suka jkai wadan nan hare hare ka iya sake kai wasu sabbi a lokacin gudanar da bikin miki mulki da ake sa ran gudanarwa a kwanaki biyar masu zuwa Idan Allah ya kaimu a birnin na Bagadaza.

Idan dai za a iya tunawa a jiya ne kungiyyar Abu Musab An Zarqawi ta kai wasu hare haren bama bamai a garuruwan Falluja da Mosul da Baquba da kuma ramadi wanda hakan yayi sular mutuwar mutane sama da dari banda kuma wasu da suka jikkata.

Bisa kuwa wan nan aiki da Abu Musab Alzarqawi yayi ikirarin cewa kungiyar sace ta kaishi ministan tsaro na kasar ta iraqi ya tabbatar da cewa suna da masaniya na duk abubuwan dake faruwa game da kungiyyar ta Al Zarqawi a don haka suna jira ne kawai a kammala mika musu mulki su kuma subi sawun sa tare da dakile irin ayukan da suke gudanarwa.

Tuni dai dama a can baya kasar Amurka ta bayar da sanarwar ladan dala miliyan goma ga duk wanda ya kamo Al Zarqawi ko kuma yayi hanyar da aka kama shi.

A daya hannun kuma sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya tabbatar da cewa a yanzu haka dakarun sojin Amurka na fuskantar mawuyacin hali na tabbatar da tsaro a kasar sakamakon aiyukan yan fadan sari ka noke da kuma na kwanton bauna.

Mr Powell yaci gaba da cewa hakan na faruwa ne bisa rikon sakainar kashi da Amurkan tayi ga aiyukan yan fadan sari ka noken a iraqi to amma duk da haka Amurka ba zatayi kasa a gwiwa ba wajen dakile aiyukan ire iren wadan nan kungiyoyi don ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a fadin kasar ta iraqi baki daya.

Bisa kuwa ire iren wadan nan hali na rashin tsaro dake ci gaba da aukuwa a kasar ta iraqi Shugaba Bush na Amurka ya kara nanana kiran sa ga shugabannin kasashe masu fada aji na duniya dasu yarda da bukatar tura dakarun tsaro na kungiyyar Nato izuwa kasar iraqi don tabbatar da zaman lafiya da kuma doka da oda,musammma bisa la,akari da cewa yau saura kwanaki biyar a mika mulki hannun yan kasar ta iraqi.

A can baya dai shugaban gwamnatin Rikon kwarya na kasar Iyad Alawi ya taba gabatar da wan nan bukata ta neman a turo dakarun kiyaye zaman lafiyar na Nato Izuwa kasar ta iraqi.

A can baya dai manya manyan kasashe biyu na cikin kungiyyar ta Nato wato Faransa da Jamus sun hau kujerar nakin tura sojin su izuwa kasar ta iraqi wanda hakan da kuma kin shiga tawagar kaiwa iraqi harin soji shine ya haifar da rashin fahjimtar juna a tsakanin su.

To amma a yanzu komai ya fara dai daita a tsakanin wadan nan kasashe.

To amma duk da haka babbar tambaya a nan shine wadan nan kasashe biyu a yanzu haka zamu amince da wan nan bukata ta Amurka a lokacin taron kungiyyar na Nato da za a fara a karshen makon nan da muke ciki a birnin Ankara na kasar Turkiyya ko ko aa.

Ibrahim Sani.