1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

April 23, 2004
https://p.dw.com/p/BvkL
Hoto: AP

Shugaban mabiya darikar Shia mai tashe yanzu haka a iraqi, Moqtadar sadr ya gargadi dakarun sojin amurka da kada su kuskura su kaddamar da yaki kann magoya bayan sa bisa hujjar kamo shi a Garin Najaf.

Yin hakan a cewar shugaban Shiawan zai zamowa dakarun sojin hadin gwiwar yin nadama,domin a cewar sa mabiyan sa zasu dinga kaddamar da kisa na kunar bakin wake a kann dakarun sojin hadin gwiwar daya bayan daya.

Moqtadar Sadr ya fadi hakan ne kuwa yau juma,a yayin da yake gabatar da jawabin hudubar juma,a a masallacin garin Kufa wanda yake da nisan kilomita kadan daga garin Na Najaf.

Moqtadar Sadr yaci gaba da bayyanawa duniya cewa magoya bayan sa sun tabbatar masa da aniyar su na kaiwa dakarun sojin Hadin gwiwar hare hare na kunar bakin wake amma yace dasu su tsaya tukuna har zuwa wani lokaci domin daukar wan nan mataki a yanzu haka baima taso ba tukuna.

Haka kuma Moqtadar Sadr yayi Allah wadai da harin bom din nan da aka kai a garin Basra,wanda sakamakon haka mutane fararen hula 73 suka rasa rayukan su,banda kuma da dama da suka jikkata.

Yin Allah wadai da wan nan abu daya faru a garin na Basra da Moqtadar Sadr yayi a cewar bayanai da suka iso mana nada nasaba ne da barnar da hakan yayi kann mutane fararen hula yan kasar ta iraqi.

Rahotanni dai a yanzu haka sun shaidar da cewa dakarun sojin na Amurka na nan jibge a wajen garin na Najaf suna jiran umarni daga sama don afkawa garin da sunan maganin masu tsattsauran raayin darikar ta shia a hannu daya kuma da kamo shugaban Moqtadar Sadr.

A yayin da ake cikin wan nan hali kuma a can waje daya shugaban addinai na kasar ta iraqi na nan naci gaba da tattauna hanyoyin sulhu da dakarun sojin na Amurka don samo bakin zaren warware takaddamar dake tsakanin su.

A daya hannun kuma kwamamdojin kasar ta Amurka sun shaidar da cewa a dai halin da ake ciki yanzu basu da shirin shiga cikin garin na Najaf da sunan yaki,duk kuwa da cewa mutumin da suke nema ruwa a jallo na boye a cikin garin na Najaf.

A wata sabuwa kuma a yau juma ,a fadar mulki ta Biritaniya ta shaidar da cewa tuni ta fara tattauna hanyoyin daya kamata abi domin cike gurbin da Sojojin kasar Spain da kuma na wasu kasashe zasu samar bayan janye dakarun sojin su daga kasar ta iraqi.

Kakakin fadar dai na Ingila ya karyata zargin wai kasar na nan na shirye shiryen tura karin dakarun soji 1,700 izuwa kasar ta iraqi don cike wan nan gwibi da wasu dakarun sojin kasashe zasu samar.

Haka kuma kakakin ya kara da cewa batun cike gwibin wadan nan sojoji na Spain ana tattauna shine a tsakanin kasar ta Biritaniya da kuma sauran kawayen ta da suka kaddamar da yaki kann kasar ta iraqi.

A yanzu haka dai kasashen da suka bayar da sanarwar janye sojojin su daga iraqin sun kai a kalla guda hudu,Babba kuma ta farko daga cikin su itace kasar spain sai kuma Tahailand da Hundurus da kuma El savado.

Shi dai faraminista Luis Zapatero na Spain yace kasar sa ta dauki wan nan matakin bisa hasashen cewa kasar Amurka bata da shirin mikawa mdd tafiyar da harkokin kasar ta iraqi a lokaci na nan kusa. Kuma ma idan hakan ya faru a cewar Zapatero to babu shakka dakarun sojin na Amurka ba zasu dinga sauraron umarni ba daga mdd sai dai daga kwamandojin su wanda yin hakan a cewar sa na a matsayin har yanzu ba a rabu da bukar ba.

IBRAHIM SANI.