1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

April 16, 2004

JAPANAWA NA MURNA NA SAKO MUTANEN SU UKU DA YAN FADAN SARI KA NOKE SUKAYI GARKUWA DASU.

https://p.dw.com/p/Bvkd
Hoto: AP

Rahotanni daga kasar ta Iraqi sun shaidar da cewa koda a daren jiya juma,a sai da akayi wata arangama a tsakanin dakarun Amurka da yan fadan sari ka noken a can garin falluja.

A cewar wata sanarwa data fito daga asibitin garin ta nunar da cewa mutane fararen hula yan kasar a kalla goma sha biyar ne suka rasa rayukansu ban da kuma wasu 20 da suka jikkata.

Bisa wan nan wan nan abu kuwa daya faru, Janaral din sojan Amurka Richard Myers yace tattaunawa a tsakanin shugaban rikon kwarya na iraqi Paul Bremer da shugabannin addin kasar na nan na gudana,kuma babu ko ja kwalliya zata biya kudin sabulu dangane da kawo karshen wadan nan tashe tashen hankula dake faruwa a wasu yankuna na kasar ta iraqi.

Bayanai dai a yanzu haka sun shaidar da cewa a yau juma,a an gano shugabannin addinan kasar ta Iraqi na yin tururuwa izuwa garin na falluja don saduwa da manya manyan kwamandojin kasar ta Amurka bisa manufar tattauna hanyoyin shawo kann wadan nan rikice rikice na tsawon kusan makonni biyu.

A cewar wani babban shugaba na darikar shia,Sheik Abdel Salam Al kubaissi,dakarun sojin na Amurka a yau juma a sun kyale wakilan shugabannin addinan shiga garin na falluja bisa dalilin ganawa dasu na samo bakin zaren warware wadan nan tashe tashen hankula.

Abdel salam yaci gaba da cewa babban makasudin wan nan ganawa itace a samo hanyoyin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a fadin kasar ta iraqi baki daya.

A cewar mabiyin darkar ta shia a tun makon daya gabata ne dakarun sojin na iraqi suka dage irin hare haren da suke kaiwa naba zata a garin na Falluja,bisa laakari da yawan mutane fararen hula da suka rasa ranyu a sakamakon ire iren wadan nan arangama.

A daya hannun kuma wata majiya mai karfi daga kasar ta iraqi ta tabbatar da cewa koda a yau juma a sai da dakarun hadin gwiwar sukayi bata kashi da yan fadan sari ka noken a garin na Falluja.

A yanzu haka dai rahotanni daga garin Najaf sun tabbatar da cewa har yanzu magoya bayan Moqtadar Sadr ne keci gaba da rike akalar tsaro na tsakiyar garin,bisa umarnin na hannun daman shugaban darikar ta shi a kasar ta iraqi.

Bugu da kari Rahotannin sun nunar da cewa a yanzu haka dakarun sojin na Amurka na can sunyi cincirindo a wajen garin na Najaf suna jiran umarnin kaddamar da farautar tsageru magoya bayan na hannun daman shugaban na shia da kuma shi kanshi Moqtadar Sadar din.

Bisa laakari da irin wan nan mataki kuwa na jibge dakarun sojin da hakan ka iya haifarwa a nan gaba,wasu manya manyan sojojin kasar Poland dake garin na Najaf sun nuna bacin ransu dangane da wan nan mataki da dakarun sojin na Amurka suka dauka.

Shi kuwa Moqtadar Sadr ,mutumin da dakarun sojin Amurkan ke nema ruwa a jallo wanda a yanzu haka ke garin na Najaf ya tabbatar da cewa kama shi ko kuma daya daga cikin jamian sa daga bangaren dakarun sojin na Amurka babu shakka abune da zai dawo da hannun agogo baya dangane da harkokin tabbatar da tsaro a kasar ta iraqi.

A waje daya kuma bayanai daga kasar ta iraqi sun shaidar da cewa japanawan nan guda uku da yan fadan sari ka noken kasar ta iraqi suka sako bayan garkuwa da sukayi dasu,a yanzu haka suna wani asibitin kasar amurka dake birnin Dubai don a duba lafiyar su kafin su wuce izuwa gida Japan.

Wadan nan mutane uku biyu maikatan bayar da agajin gaggawa dayan kuma dan jarida mai daukar hoto yan fadan sari ka noken na iraqi sunyi garkuwa dasu ne tare da wasu na kasashen waje bisa bukatar neman dakarun sojin hadin gwiwar ficewa daga kasar ta iraqi.

IBRAHIM SANI.