1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A KASAR IRAQI.

July 21, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhv

Rahotanni daga kamfanin dillancin labaru na reuters,ya bayyana cewa a yau laraba wani reshen kungiyar alqaeda a kasashen turai,sun gargadi yan kasashen bulgaria da poland da su janye dakarun sojin su daga kaga kasar iraqi.

Kasashen biyu,sun samu wannan gargadi ne ta hanyar yanar gizo,inda wannan kungiya ta gargade su dasu yi gaggawar daukar matakan janye dakarun su daga kasar iraqin,ko kuma su fuskanci irin harin da aka kai wa amurka na sha daya ga watan satumba.

Ita dai kasar bulgaria,kungiyar yan tawayen a cikin kurarin ta ga kasar ta yi ikirarin mai da kasar bulgariya magudanar jini muddin basu janye dakarun sojinsu daga iraqi ba.

Ita kuwa kasar poland,a gargadin daya iske ta,ya nemi prime ministern kasar Marek Belka daya hanzarta janye sojin sa daga iraqi,ko kuma su farma kasar sa da hare haren boma bomai.

A yan makwannin nan dai,irin wannan barazana ta zama ruwan dare ga kasashen ketare da ke da dakarun sojin su a kasar ta iraqi,hakan kuwa ya sa kasar bulgaria,tace baza ta dauki wani mataki ba har sai ta samo silar wannan barazana.Maana,sai ta tabbatar da wanda ya aiko da wannan sako.

Shi kuwa mukaddashin ministern tsaro na kaasar poland,Janusz Zemke,cewa yayi kasar poland tana jira ne taji shawarar da sauran kasashe zasu yanke a kann matakin daya kamata a dauka.

Rahotanni a jiya talata sun bayyana cewa wani sako daya iske kasar japan ta yanar gizo,ya gargadi kasar data janye dakarun sojin ta dari biyar da hamsin daga kasar iraqin,wannan sako dai kamar yadda kasar japan din ta samu ya fito ne daga kungiyar tawaye dake karkashin jagorancin Abu-Musab Al Zarqawi,wanda kuma daga baya kasar ta sake samun sakon cewa,wannan gargadi na karya ne.

Bisa irin wannan ne kasashen biyu suke jiran tabbacin sakon kafin su dauki mataki,a yanzu haka dai kasar bulgaria tace wannan barazana baza ta sa ta janye sojin ta dari hudu da sabain ba dake kasar ta iraqi,duk kuwa da cewa tuni yan tawayen suka halaka dan kasar bugarian guda daya.Ita kuwa kasar poland a yanzu haka tana da dakarun sojin ta har mutum dubu biyu da dari hudu a kasar iraqin.

A yau ne kuma wannan dan kasar phillipine din da yan tawayen suka yi garkuwa da shi kwanakin baya zai bar kasar iraqin izuwa gida,bayan da shugabar kasar phillipine Gloria Aroyo,ta mika wuya ga yan tawayen ta hanyar bin raayin su,wajen janye dakarun kasar ta daga iraqin.

Kasashe da dama musamman ma kasar amurka da australia,sun yi suka ga wannan mataki da shugaba Gloria Aroyo ta dauka,wanda suka ce hakan zai karawa yan tawayen kwarin gwiwa wajen gudanar da taaddancin su.

Shi kuwa kakakin shugabar kasar phillipines Ignacio Bunye,ya tabbatar da cewa shugaba Aroyo ko kadan bata dana sanin wannan mataki data dauka,a hannu daya kuma kasar ta phillipine bata da niyyar canza dangantakar dake tsakanin ta da kasar amurkan.

Maryam L.Dalhatu.