1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Kongo shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus

June 4, 2004

A wannan makon dai sabbin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a gabacin kasar Kongo shi ne ya mamaye kanun rahotannin jaridun Jamus akan al'amuran Afurka

https://p.dw.com/p/Bvpv
'Yan gudun hijira dake kaura zuwa Ruwanda sakamakon tashe-tashen hankula a Bukavu ta gabacin Kongo
'Yan gudun hijira dake kaura zuwa Ruwanda sakamakon tashe-tashen hankula a Bukavu ta gabacin KongoHoto: AP

Muhimmin abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon shi ne sabon fadan da ya sake barkewa a gabacin kasar Kongo, inda jaridar DIE TAGESZEITUNG take cewar:

"A daidai ranar da aka tsayar domin bikin nadin sabon gwamnan lardin gabashin Kongo aka shiga wani sabon hali na kaka-nika-yi kuma ba wanda ya san yadda makomar yankin zai kasance sakamakon kazamin fadan da ake gwabzawa tare da ‘yan tawaye masau ta da kayar baya. Wannan dai shi ne fada mafi muni da aka fuskanta a kasar ta Kongo tun bayan nadin gwamnatin hadin gambiza da aka yi a kasar shekarar da ta wuce. Sama da farar fula dubu uku suka tsere zuwa Ruwanda, wasu daga cikinsu dauke da munanan raunuka."

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG a lokacin da take ba da wannan rahoto ta lura ne da hujjar da ‘yan tawayen suka bayar dangane da wannan bore nasu, inda ta kara da cewar:

"Bisa ta bakin ‘yan tawaye masu tayar da kayar baya a sabon fadan da ake fama da shi a gabacin Kongo yanzu haka shi ne, wai sun dauki wannan mataki ne domin kandagarkin wata makarkashiyar kisan kiyashin da aka kulla akan ‘yan kabilar Tutsi dake wannan yanki. Fadawa hannun ‘yan tawaye da garin Bukavu, shelkwatar yayi ka iya hana ruwa gudu ga hada-hadar neman zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar ta Kongo da ake famar yi."

A can kasar Sudan har yau ana ci gaba da fama da rikici, wanda ke barazana ga makomar hadin kan wannan kasa da ta fi kowace girma a nahiyar Afurka. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU tayi nuni ne da cewar:

"Ga alamu dai tarihi ne yake maimaita kansa. Domin kuwa a zamjanin baya Larabawa kan kutsa kai yankin kudancin Nilu ne domin wawason ganima, inda suka fi mayar dahnakali akan cinikin bayi, amma a yanzun nema suke yi su dora hannu akan arzikin man fetur. Wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya fadar mulki ta Khartoum ta amince da zaman yarjejeniyar zaman lafiyar da ta tanadi kwarya-kwaryan ikon cin gashin kai ga lardin kudancin Sudan. Amma fa tilas ne gwamnati tayi taka-tsantsan ta la’akari da barazanar wargajewar kasar ta Sudan baki daya sakamakon ballewar lardin kudancinta da kuma tawayen da ake fama da shi a Darfur a yammaci da kuma lardin gabacinta a iyaka da kasar Eritrea."

Kasar Botswana dake makobtaka da Zimbabwe ta fara shingence iyakokinta domin hana tuttudowar bakin haure daga makobciyar tata. Mujallar FOCUS tayi bitar lamarin ta kuma ci gaba da cewar:

"A cikin wata sanarwar da ta bayar a hukumance kasar Botswana zata shingence iyakokinta mai tsawon kilomita 500 da makobciyarta Zimbabwe, wai saboda kare shanunta daga cututtukan dabbobi daga Zimbabwen. Tuni dai aka kammala kafa shinge mai nisan kilomita 300 da kuma tsawon mita biyu da rabi a iyaka tsakaninta da Zimbabwe. Amma fa a hakikatal-amari wannan mataki, a daya bangaren, na da nufin hana tuttudowar bakin haure daga kasar Zimbabwe mai fama da matsalolin tattalin arziki zuwa karamar kasar Botswana dake samun bunkasar tattalin arzikinta. Alkaluma sun ce kimanin bakin haure dubu dari ne kan tsallaka daga Zimbabwe zuwa Botswana a wata sakamakon tabarbarewar al’amura da kuma rashin guraben aikin yi a kasarsu."

Kasar Amurka ta tashi haikan wajen neman cin gajiyar arzikin man fetur da Allah Ya fuwace wa nahiyar Afurka, a cewar jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU a cikin wani dan takaitaccen sharhin da ta gabatar, inda ta ci gaba da cewar:

"A sakamakon hali na rashin sanin tabbas da ake ciki a mashigin tekun Pasha kasar Amurka ke neman sassauta dogaro da take yi wajen samun man fetur daga wannan yanki. Kimanin dala miliyan dubu 60 Amurka ke da niyyar zubawa a harkar hakan man fetur a nahiyar Afurka a cikin shekaru masu zuwa. To sai dai kuma abin haufi a nan shi ne kasancewar talakawa ‘yan rabbana ka wadatamu a nahiyar ba zasu ci gajiyar wannan sabon ci gaba ba."