1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Lebanon

August 1, 2006
https://p.dw.com/p/BuoD

Ana cigaba da gwabza faɗa tsakanin Israila da dakarun Hizbullah a kudancin Lebanon. A ranar Talatan nan Israila ta fadada farmaki da kuma kutsen da take yi, inda ta rika luguden wuta a ƙauyukan kan iyaka a kudancin Lebanon. A irin turjiyar da sojin Israilan ke fuskanta, dakarun Hizbullah sun kashe sojojin Israilan uku. Faɗan wanda ya ɓarke bayan sace wasu sojojin Israila biyu da yan Hizbullah suka yi ya shiga mako na uku ba tare da ƙaƙƙautawa ba. Majalisar zartarwar Israila ta baiwa sojojin ta umarnin faɗaɗa farmaki ta ƙasa. Ƙasar ta Israila ta ce zata cigaba da farmakin jiragen sama a ranar Laraba bayan ƙarewar waádin saói 48 na tsagaita kai farmakin ta sama. Sojin Israilan sun gargaɗi mazauna yankunan dake arewacin Lebanon da su ƙauracewa wannan wuri saboda hare haren da za su kai, ka iya nesawa fiye da waɗanda suka wakana a baya. Ministan lafiya na ƙasar Lebanon yace a ƙalla mutane 750 suka rasa rayukan su tun bayan ɓarkewar faɗan. Yayin da a nata ɓangaren Israila ta bada sanarwar cewa an kashe mutanen ta 51.