1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A LIBERIA

ZAINAB AM ABUBAKARDecember 2, 2003
https://p.dw.com/p/BvnI
A jiya litinin ne aka kaddamar da wani shirimn karban makamai daga hannun yan tawayen Liberia kimanin dubu 40,domin sanyasu cikin jamaa bayan yake yake da suka sha gwabzawa na tsawon shekaru 14 da suka gabata.

Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Liberia Gyude Bryant ya bayyana cewa hakan nada nufin lalata wadannan makaman tare da sake shigar dasu cikin harkoki na yau da kullun na wannan kasa.Shugaban gwamnatin ya fadawa majalisar dunkin duniya wadda ke tafi da wannan campaign cewa gwamnati ta basu goyon bayanta dari bisa dari .

A yakin na kasar Liberia dake yammacin Afrika sama da mutane dubu 200 suka rasa rayukansu tun daga shekara ta 1989,ayayinda kowane kashi daya daga cikin biyar na mutanen kasar suka rasa muhallinsu ,wadanda ayanzu haka ke gudun hijira a wasu garuruwa na cikin kasar ko kuma wajenta. A watan Augustan daya gabata aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a wannan kasa mai yawan jamaa million 3 da dubu dari 3,bayan madugun yan tawaye kuma tsohon shugaban Liberia Charles Taylor ya bar kasar domin gudun hijira a tayyara Nigeria.

Mayakan tsohon shugaban Liberia Taylor dai sun bayyana muradinsu na ajiye makamai,inda kimanin 700 daga cikinsu suka mika kayan fada guda 300.Da kashi daya daga ciki ukun dakarun kiyaye zaman lafiya dubu 15 na mdd a wannan kasa a yanzu haka,babu alamun kalubalantar mayaka dubu 40 dake wannan kasa,mayakan dake dari darin mika makaman nasu domin rashin sanin makomarsu a wannan kasa nan gaba musamman a dangane da matsalar rashin aikinyi.A halin da ake ciki yanzu haka dai ana kyautata zaton cewa da zarar kimanin mayakan dubu 15 wadanda shekarunsu bai wuce 18 sun mika makaman nasu,zaa bude musu cibiyoyi na shawarwarin yadda zasu tafi da harkokinsu da kuma basu dala 300.

To sai dai ana dara ga dare yayi,ayan makonni biyu da suka gabata wasu mayakan da suka mika wuya tare makaman nasu basu samu shawarwari balle kudi da aka alkawarta ba,ayayinda abinci da aka musu alkawari na nan kulle har yanzu. Amma kakakin dakarun kiyaye zaman lafiya Patrick Coker ya sanar dacewa har yanzu baa tura sojojin majalisar zuwa yankunda dake hannun yan tawayen LURD mafi girma a wannan kasa ba.

A halin yanzu dai kasashe da dama sun nuna goyon bayansu wajen tallafawa Liberia warware rikicin karban makaman yan tawayen,tare da sake farfado da wannan kasa,bayan yake yaken shekaru 14.