1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

halin da ake ciki a Pakistan

Yahouza S.MadobiJuly 9, 2007

Rikici ya ƙi ci ya ƙi cenyewa a Lal Massajid na birnin Islamabad

https://p.dw.com/p/Btv5
Hoto: AP

Kaɗan kenan daga karan bingigogi a rikicinda ya ki ci ya ki cenyewa,tsakanin dakarun gwamnatin Pakistan, da wasu yan takife, da su ka yi kaka gida, a cikin Lal Masajid, ko kuma Jan massalaci dake birnin Islamabad.

Wannan yan takife masu alaƙa da ƙungiyar Alqa´ida, sun yi garkuwa da ɗaruruwan mata da ƙananan yara, da ke cikin massalacin.

A halin da ake ciki, wani komitin manyan mallumai masu faɗa a ji na ƙasar Pakistan, sun shiga tsakani, domin lalashi yan takifen su fita daga harabar Lal massajid.

Shugaba Pervez Musharaf na Pakistan, ya bayyana yiwuwar baiwa dakarun gwamnati izinin kai wani gagagarmin hari domin kawa ƙarshen wannan rikici:

„ ya zama wajibi ga yan takifen su fito, su kuma miƙa wuya.

A game da haka ina mai gargaɗi zuwa gare su: Idan ba su bada kai ba bori ya hau,tamkar sun sayi mutuwa ne da kuɗin su.

A yanzu, haƙurin mu ya kai ƙarshe.

Babu shaka, a ɗaya hannun, mu na tare da zullumi da kuma tausayi a kan mata da ƙananan yara da ke ciki wannan massalaci“.

A yayin da manyan mallumai su ka shiga tantanwar magance rikicin, shugaba Pervez Musharaf na ci gaba da ganawa da muƙƙaraban sa, a game da mattakan abkawa masalacin hari muddun shiga tsakanin ba ta yi nasara ba.

To saidai da dama daga al´ummomin Pakistan, na adawa da matakin na shugaban ƙasa, kamar yadda Munawar Hassan shugaban ƙungiyar addini ta MMA ya bayyana.

„Babu mutumen da zai bada goyan baya da ga harin da sojojin gwamnati ke shirin kai waga masalacin.

Abun takaici a ƙasar Pakistan shine,sojoji mamaikon su zama garkuwa , har kullum su ne ummal ibasar bila´o´in da al´umma ke fuskanta.

A yankin Bajour da ke matsayin sanssanin mabiya aƙidar taliban dubbunan jama´a, dauke da bingigogi da kulake,sun shirya zanga-zanga, a yau litinin, domin nuna goyan baya ga yan takifen massalacin Lal Massadjid.

Sun kuma yi ta rera kalamomi masu Allah wadai ga shugaban Musharaf, tare da ɗaukar aniyar shiga yaƙin jihadi.

A ɗaya wajen, jama´iyun adawar Pakistan, sun shirya wani taron gangami a birnin London jiya lahadi, inda su ka kiri shugaba Pervez Musharaf ya yi murabus daga muƙamin sa.