1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki A sudan shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus

May 14, 2004

Masharhanta na jaridun Jamus sun ci gaba da sukan lamirin kungiyoyi na kasa da kasa a game da rikon sakainar kashin da suke wa rikicin Darfur a yammacin Sudan

https://p.dw.com/p/Bvpy
Rikici a yammacin Sudan
Rikici a yammacin SudanHoto: AP

Hatta a wannan makon dai, daidai da sauran makonni biyun da suka wuce, halin da ake ciki a yammacin kasar Sudan shi ne ya fi ci wa masharhanta na jaridun Jamus tuwo a kwarya. Misali jaridar DIE WELT a lokacin da take gabatar da nata sharhin cewa tayi:

"Tun shekaru gommai da suka wuce kasar Sudan take fama da yakin basasa tsakanin sojojin gwamnatin tsakiya ta Musulmi a arewaci da ‘yan tawayen SPLA da aka ce wai Kiristoci ne a can kudancin kasar, wanda kuma yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da miliyan biyu. Kasar kazalika har yau tana fama da matsalar nan ta cinikin bayi kuma rikicin da ake fuskanta a Darfur abu ne dake yin nuni da salon tunanin Larabawa jajayen fatu dake ganin fifikon kansu akan ‘yan-uwansu Musulmi bakar fata. A sakamakon ta da kayar baya da bakar fatar suka yi a misalin shekara daya da ta wuce, gwamnati a fadar mulki ta Khartoum ta ba da umarnin killace lardin baki daya ta kuma tura dakarunta ‘yan sa kai su bannatar da kauyukan yankin su kuma fatattaki mazauna cikinsa. Dukkan wadannan abubuwa na faruwa ba tare da kungiyoyi na kasa da kasa irinsu MDD ko Kungiyar Tarayyar Turai sun dauki wani mataki na dakatar da ta’asar ba. Ita kanta Kungiyar Tarayyar Afurka ta gaza, kazalika Kungiyar Hadin kan Larabawa, saboda babu daya daga cikinsu da ta fito fili tayi Allah Waddai da mummunan ci gaban da ake samu na kisan kare dangi a lardin Darfur a yammacin Sudan."

Ita ma jaridar Frankfurter Rundschau ta bayyana mamakin yadda Kungiyar Tarayyar Afurka ta zura na mujiya tana kallon ta’asar dake wanzuwa a Darfur ba tare da ta ce uffan ba. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Ga alamu dai canjin suna ne kawai aka samu daga Kungiyar Hadin Kan Afurka OAU zuwa Kungiyar Tarayyar Afurka AU, amma in banda hakan babu wani sauyi da aka samu a game da surutai na fatar baki da aka saba ji daga bakin shuagabannin kasashenta ba tare da sun tabuka kome ba. Kungiyar, wacce aka canza mata suna shekaru biyu da suka wuce, ba abin da ta tabuka domin dakatar da rikicin kasashen Liberiya da Cote d’Ivoire, kuma hakan shi ne ke faruwa dangane da kasar Sudan, duk kuwa da ikirari da kuma cika bakin da shuagabannin suka yi na katsalandan a rikice-rikice da kashe-kashe na kare dangi a nahiyar Afurka."

Gwamnatin Afurka ta Kudu ta ba da kai bori ya hau dangane da bukatun kungiyoyin taimakon jinkai domin raba magungunan cutar kanjamau kyauta ga majiyyata. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Neues Deutschland cewa tayi:

"Bayanai da aka tara sun nuna cewar kimanin kashi daya cikin tara na illahirin al’umar ATK su miliyan 43 ke dauke da kwayar cutar Aids mai karya garkuwar jikin dan-Adam. Cutar ba ta bar kowa ba ta hada ne da dukkan jinsuna da kabilun kasar ta kan kuma rutsa da mutane 600 a rana. Mata dai sune suka fi zautuwa. Ta la’akari da haka kungiyoyin taimakon jinkai suke madalla da amsa kiransu da gwamnati ta yi wajen raba maganin cutar kyauta a tsakanin majiyyata saboda ta haka ne za a sassauta musu radadinta. To sai dai kuma duk da wannan kykkyawan ci gaba ana tababa a game da samuwar karin masu kamuwa da kwayoyin cutar ta Aids dake barazana ga makomar tattalin arzikin kasar ta ATK."

Ita ma jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar matsalar ta cutar Aids dake nema ta zame wa kasashen Afurka kayar kifi a wuya. Jaridar ta ambaci gargadin da kungiyar lafiya ta duniya WHO tayi sai ta kuma kara da cewar:

"Kasashen Afurka na fuskantar barazanar gurguncewar tattalin arzikinsu kwata-kwata, muddin ba a dauki nagartattun matakai na gaggawa domin shawo kan yaduwar cutar nan ta Aids ba, fiye ma da ire-iren hasashen da aka yi a zamanin baya. A halin yanzu haka cutar ta Aids ita ce babban ajalin mamata dake da shekaru tsakanin 15 zuwa 59 da haifuwa."