1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu na fuskantar fashi da makami

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 23, 2015

'Yan fashi da makami a Sudan ta Kudu sun addabi kungiyoyin bayar da agaji da ke tallafawa al'ummar kasar da yaki ya dai-daita.

https://p.dw.com/p/1HAxQ
Hoto: Getty Images/AFP/N. Sobecki

Rahotanni sun nunar da cewa ma'aikatan bayar da agaji na kasa da kasa da ke tallafawa mutanen da ke cikin tsananin bukatar taimako a kasar ta Sudan ta Kudu na fuskantar hare-hare daga 'yan fashi da makamai a sassa daban-daban na kasar. Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa hari na baya-bayan nan shi ne wanda wasu mutane dauke da bindigogi suka kai wa ma'aikatan kungiyar ba da agaji da kasar mai suna Nile Hope, tare da sace musu kayayyakin da suke rabawa na agaji. Majalisar ta kara da cewa kungiyoyin ba da agajin sun bayar da rahotannin hari na fashi da makami har sau 32 cikin watan Oktoban da ya gabata kdai, ciki kuwa har da guda 15 da aka kai musu a babban birnin kasar Juba. Sudan ta Kudu dai ta fada cikin rudani sakamakon fadan kabilanci tsakanin magoya bayan shugaban kasar Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar wanda ya rikide zuwa yakin basasa.