1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a tsibirin Lampedusa

Awal, MohammadJanuary 27, 2009

Halin da ake ciki game da matsalar baƙin haure ya ƙara dagulewa a tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya.

https://p.dw.com/p/GhEQ
Zanga-zangar ´yan ci-rani a LampedusaHoto: picture-alliance / dpa

A yanzu haka ministan cikin gidan Italiya zai kai ziyara zuwa ƙasar Tunisiya a ƙoƙarinsa na samun mafita daga wannan matsala.

Sabon bori da aka tayar a tsibirin Lampedusa ya ƙara taɓarɓarar da halin rayuwar jama'ar da ke zaune a wannan wuri inda al'umar yankin ke gudanar da zanga zanga don nuna rashin amincewa da matakin kafa wuraren tsare baƙin haure da ke sulalewa zuwa wannan yanki ta kwale kwale da ministan cikin gidan Italiya ya ba da sanarwarsa a ranar Juma´a da ta gabata da nufin kare gidajen yarin da ke tsibiran wannan ƙasa.


A ranar Alhamis ne ministan cikin gidan Italiya Roberto Maroni zai kai ziyara zuwa ƙasar Tunisiya inda zai tattauna tare da takwaransa akan amfani da kwale kwale da baƙin hauren ke yi daga Tunisiya zuwa tsibirin na Italiya. A tattaunawarsa da mahukuntan Tunisiya ana sa ran cewa Maroni zai samar da wani abu mai ɗorewa da zai magance wannan matsala. An nunar da cewa akasarin mutanen da ake tsare da su a Lampedusa sun sulalo ne daga ƙasar ta Tunisiya. Ana hasashen samun tashe tashen hankula da zaran an bayyanar da sakamakon tattaunawar sabo da cewa bisa ga dukkan alamu Italiya tana shirin komawa da mutane da dama ƙasashen na asali. A don haka ne ma wasu mata 20 suka shiga yajin ƙin cin abinci.

Valerio Neri shugaban ƙungiyar Save the Children da a halin yanzu ita ce kaɗai ƙungiyar da ke aikin ba da agaji a sansanonin baƙin hauren da ke Lampedusa ya soki matakin tsare mutane da dama da suka haɗa da matasa maza da mata da aka shafe kwanaki ana yi a wannan wuri inda ya ke cewa.

"A ganina wannan mataki ba zai taimaka ba sabo da cewa akwai haɗarin tafka kuskure sakamakon yin garaje wajen gano mutane. Alal misali idan aka kuskure mai shekaru 17 da haifuwa aka ɗauke shi tamkar mai shekaru 21 to za a iya korarsa daga tsibirin, ba tare da an san inda ya dosa ba. Ka ga kenan hakan ya zamo take haƙƙin bil Adama.

Ma'aikatar cikin gidan Italiya ta musunta rahotanni dake nuni da cewa akwai baƙin haure da dama da ake tsare da su a sansanonin. A ƙarshen makon da ya gabata sai da ɗaruruwan baƙin hauren suka gudu daga inda ake tsare da su. A cewar wani ɗan jarida na wannan ƙasa ba a da masaniya game da matsalar da baƙin haure ke fuskanta sakamakon yadda ake garƙame ƙofofin sansanonin da ake tsare da su.

"Ya ce an garƙame tsibirin kuma babu hanyoyin kaiwa wannan wuri. A don haka rufe sansanonin abu ne da ba zai yi matuƙar wuya."

Ba a gano takamammen dalilin da ya sa mahukunta suka ɗau wannan mataki ba. Watakila hakan na da nasaba da jawabin da firaminista Silvio Belusconi ya yi a ƙarshen makon da ya gabata cewa baƙin hauren sun shiga garni ne domin su dan shaƙata. Babban limamin kirista na wannan tsibiri Stefano Nasatasi ya yi tsokaci game da wannan kalami inda ya ce.

"Mu dai a hakika ana mayar da mu saniyar ware saboda an keɓe mu daga sauran sassan ƙasar da kuma duniya baki ɗaya. Halin da muke ciki wani abu ne mai kama da mamaya."

A halin yanzu ´yan gudun hijira kimanin dubu guda da ɗari uku ke zaune a sansanonin guda biyu da ke da nauyin ɗaukar mutane ɗari tara. Akwai kuma masu neman mafakar siyasa kimanin ɗari da aka amince da takardunsu na neman mafakar siyasa. A yammacin jiya Litinin aka wuce da su zuwa garin Bari domin basu takardar shedar matsayinsu.