1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a yankin Darfur na kasar Sudan--

Jamilu SaniJune 4, 2004

Kungiyoyin kare hakin bil adama na duniya sun zargi gwamnatin Sudan da laifin kisan fararen hula da ake yi a yankin Darfur----

https://p.dw.com/p/Bvj8
Hoto: AP

Ta la’akari da tashe tashen hankulan dake faruwa a yakin Darfur na kasar Sudan,kowa na iya tabatar da gaskiyar cewar barkwar irin wadanan tashe tashen hankula na barazana da rayuwar alumomin wanan yanki na Darfur da yawan su ya kai miliyan biyu,koda yake gwamnatin Sudan ta amince kungiyoyin bada agaji na duniya su cigaba da gudanar da aiyuka na jin kai a yakin Darfur,to amman kuma kungiyoyin kare hakin jama’a na duniya na KIRA ne ga gwamnatin Sudan data tabatar da tsaron lafiyar fararen hular wanan yanki.

Masana aiyukan bada agaji na duniya,sun kiyasta cewar fiye da mutane 300,000 zasu iya rasa rayukan su a yakin na Darfur sakamakon tashe tashen hankulan da suka barke a wanan yanki,baya kuma ga matsaloli na rashin issahen abinci da ake fama da shi a tsakanin haulolin dake zaune a yankin na Darfur.

Kungiyar nan ta kare hakin bil adama ta kasa da kasa ta Amnesty International dake da mazauni a birnin London, ta zargi mayakan kungiyar yan tawaye ta Janjaweed dake samun taimakon gwamnatin Sudan da laifin keta hakokin bil adaman dake faruwa a yakin Darfur,inda suka rika kai hare hare kann duban alumomin dake zaune a yankin Darfur na yankin arewa maso yammacin Sudan.

Bugu da kari wata kungiyar kuma ta kare hakin bil adama ta human Rights Watch mai hedkwata a kasar Amurka,ta zargi gwamnatin Sudan da laifin ingiza wutar rikicin kabilancin da ya barke a yankin Darfur a tsakanin hauloli ukun dake zaune a wanan yanki.

Irin wanan hali dai na barkewar tashe tashen hankula na kabilanci a yakin Darfur,ya jefa alumomin yankin da yawan su ya kai miliyan biyu ko kuma kashi uku na mazauna yankin cikin hali na kaka ka yi,don haka ne ma ofishin dake lura da aiyukan bada agaji na kungiyar hadin kann turia ya kiyasta cewar ya nuna matukar damuwarsa da halin da ake ciki a yankin na Darfur.

Sakamkon barkewar wadanan tashe tashen hankula a yankin na darfur,kimanin mutane 750,000 ko kuma miliyan daya dake zaune a yankin na Darfur ne suka shiga gudun hijira a kasar Chadi mai makwabtaka da Sudan.

A yau alhamis ne dai kungiyoyin kare hakin jama’a ke suka halara a birnin Geneva,don halartar taron kasahe masu bada taimako ga yankin na Darfur,wanda kuma majalisar dikin duniya,Amurka da kuma kungiyar hadin kann turia suka dauki nauyin gudanar da shi.

Jan Egeland daractan aiyukan bada agaji na majalisar dinkin duniya,ya kiyasta cewar ana bukatar akala dola miliyan 236 wajen gudanar da aiyuka na jin kai a yakin Darfur,inda ake fatan za’a yi amfani da irin wadanan kudade wajen sayen abinci,magunguna,samar da gidaje da dai sauran su.