1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A YANKIN DARFUR NA KASAR SUDAN

YAHAYA AHMEDMay 10, 2004

Ana dai faragabar cewa, halin kaka ni ka yi da `yan gudun hijira ke huskanta a yankin Darfur zai iya kara tabarbarewa, idan ba a dau mataki cikin gaggawa ba. Jami'ar gwamnatin tarayyar Jamus, Kerstin Müller ce ta bayyana haka, bayan dawowarta daga ziyara a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/Bvjm
Yana kanana `yan gudun hijira, daga yankin Darfur, a kan hanyarsu zuwa Cadi.
Yana kanana `yan gudun hijira, daga yankin Darfur, a kan hanyarsu zuwa Cadi.Hoto: AP

Jami’ar gwamnati Kerstin Müller, ba ta fito fili ta ce ana kisan kiyashi a yankin Darfur ba. Amma duk bayanan da ta yi wa maneman labarai na nuna cewa, kusan hakan ne ke wakana a wannan yankin na yammacin kasar Sudan. A nata ganin dai:-

"Abin da ke aukuwa a yankin dai, wani mummunan kalubale ne da ya taba shafar halin rayuwar dan Adam a duniya, wanda kuma kamar yadda nake gani, zai iya habaka ya zamo wata gagarumar annoba. A sansanonin da muka ziyarci dai, babu wadanda ake gani sai `yan bakaken fata, wadanda ke bayyana cewa, dakarun kabilun Larabawa na janjaweed ne suka kore su daga matsugunansu."

A yankin na Darfur dai, an kiyasci cewa, kusan `yan gudun hijira miliyan daya ne aka tilasa musu kauracewa daga matsugunansu. Kerstin Müller ta bayyana cewa, kusan mutane dubu 10 ne suka rasa rayukansu. Wadanda suka sami damar tsallakewa zuwa kasar Cadi ne kawai, za su iya cewa sun tsira daga hannun mayakan kabilun Larabawar nan na Janjaweed. Jami’ar ta gwamnatin tarayya, ta ci gaba da bayyana cewa:-

"A kasar Cadi a halin yanzu, akwai `yan gudun hijira kusan dubu dari da 25, mafi yawansu kuma, mata ne da yara kanana. Sansanin da suke dai ya cika ainun. Ba za a iya karbar sabbin `yan gudun hijira nan ba. Ana kokarin gina wani sabon sansanin kafin damina ta fara."

Tun karshen shekarar bara ne rikici ya barke a Yammacin Sudan. Su dai `yan bakaken fata da ke zaune a yankin Darfur sun sami kansu ne cikin wani hali na kaka ni ka yi, sakamakon afka musu da dakarun gwamnatin Sudan da `yan kurarsu, wato mayakan kabilun larabawan Janjaweed, suka yi. Kamar dai yadda Müller ta bayyanar:-

"Babu shakka, mayakan janjaweed din, suna hadin gwiwa ne da gwamnatin Sudan, wadda take ba su makamai. Bugu da kari kuma, mun sami labaran cewa, dakarun gwamnatin ne ke fara kai hare-haren bamabamai da jiragen sama a yankin. Daga bisani ne kuma, mayakan janjaweed din ke bi ta kasa su afka wa bakaken fatan, su kore su, sa’annan su cinna wa gidajensu wuta."

Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Sudan da `yan tawayen yankin na Darfur, ba ta da wani amfani, saboda babu mai kiyaye ka’idojinta. kungiyoyin ba da taimakon agaji na kasa da kasa kuma, ba sa samun izinin shiga yankin don ba da taimako. Sabili da haka ne dai, jami’ar ta gwamnati ta ga ya kamata, a angaza wa bangarorin biyu, don su bai wa masu ba da taimakon agajin damar kai ga wadanda suka fi bukatar taimakonsu.

Kungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, ta ce za ta fara tura masu sa ido ne a Sudan, don su lura da yadda ake kiyaye ka’idodjin tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu. Ta dai sami goyon bayan Kungiyar Hadin Kan Turai, wadda ta ce za ta ba da taimakon kudi da jami’ai. A halin yanzu dai, jami’ar gwamnatin tarayyar Jamus da ta ziyarci yankin na Darfur, Kerstin Müller, ta ce babu wata bukatar tura dakaraun kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin.