1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Zimbabwe

Tanko Bala, AbdullahiJune 23, 2008

Siyasar Zimbabwe ya ɗauki sabon yanayi

https://p.dw.com/p/EPZr
Shugaban Adawa na Zimbabwe,Morgan Tsvangirai.Hoto: AP

Alámura na kara yin tsamari a Zimbabwe inda a yau ɗin nan 'yan sanda suka afka Hedikwatar jamíyar adawa ta MDC suka yi awon gaba da magoya bayan ta, kwana guda bayan da madugun adawar Morgan Tsvangirai ya janye daga takarar shugabancin ƙasar.

Zimbabwe.


Halin dai da ake ciki a ƙasar Zimbabwe na ɗaukar sabon salo da kuma yanayi na rashin tabbas. Yayin da shugabanin ƙasashen duniya ke cigaba da yin tofin Allah tsine ga matakan tursasawa da shugaba Robert Mugabe ke ɗauka da yin karan tsaye da haifar da ruɗani gabanin zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa da da zaá kaɗa a ranar jumaár nan mai zuwa, a waje guda kuma yan sanda na cigaba da yiwa yan adawa ɗibar karan mahaukaciya.


Ko da a yau ɗin nan yan adawan sun koka yayin da 'yan sandan dauke da kulake da barkonon tsohuwa suka afka Hediwaktar jamíyar adawar ta MDC suka yi awon gaba da jamián ta da wasu magoya bayan jamiýar da dama.


Kakakin jamíyar Nelson Chamisa yace mutanen su kimanin 80 ne 'yan sanda suka kama, yana mai cewa abin da 'yan sandan suka yi ba komai bane illa dimaucewa da gigita da gwamnatin Mugabe ta yi bayan da Madugun adawa Morgan Tsvangirai ya sanar da janyewar sa daga takarar. Tsvangirai yace karuwar tarzomar dake gudana ta sanya cewa zai yi matukar wahala gwamnatin ta gudanar da zabe na gaskiya da adalci.


Tsvangirai yace halin da ake ciki a yau ko kaɗan bai bada dama ba ta yadda zaá yi zaɓe sahihi da kowa zai amince da shi. Domin da yan banga da yan ina da yaki dama shi kan sa Mugabe sun fayyace karara cewa duk mutumin da yace zai jefa min kuriá to zai fuskanci ukuba mai tsanani ko ma ya rasa ran sa.


Sai dai kuma a waje guda duk da janyewar da Madugun adawar Morgan Tsvangirai daga shiga takarar, gwamnatin Zimbabwen tace zaá cigaba da gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara lamarin da zai baiwa Robert Mugabe mai shekaru 84 a duniya damar cigaba da kasancewa a karagar mulki.


Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya baiyana janyewar Tsvangirai daga takarar da cewa babban abin bakin ciki ne ga dimokraɗiyya a Zimbabwe. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice tace gwamnatin Mugabe ba zata kasance halastacciya ba, a yanayin da gwamnati ta karbi mulki ba bisa tafarkin zaɓe na dimokraɗiyya ba.


A nasa ɓangaren shugaban hukumar haɗin kan Afirka Jean Ping ya baiyana takaici da halin da ake ciki a Zimbabwe yana mai cewa ba zaá iya gudanar da zaɓe na gari a irin wannan yanayi ba. Yana mai cewa wannan hali da kuma karuwar tashe tashen hankula a Zimbabwe sun sanya kungiyar cikin damuwa matuka.


Ping yace yana tattaunawa da shugaban kasar Tanzania kuma shugaban kungiyar gamaiyar Afrika shugaba Jakaya Kikwete da sauran shugabanin kasashen kudancin Afrika SADC kan yadda zaá shawo kan rikicin zaben. Shugaban kasar Afrika ta kudu Thabo Mbeki yayi bayani da cewa .


Yace yana fata gwamnatin zata bada dama yadda zaá sami cimma yarjejeniya a game da makomar ƙasar su.


A halin da ake ciki Madugun adawar Morgan Tsvangirai ya nemi mafaka a Ofishin jakadancin Netherlands dake birnin Harare domin tsira daga farautar da gwamnatin Mugabe ke yi masa.


A halin da ake ciki Ministocin harkokin waje na ƙasashen kudancin Afrika na gudanar a ƙasar Angola domin gano bakin zaren warware badakalar siyasar ta Zimbabwe.