1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Zimbabwe

December 23, 2009

Sakamakon daidaituwar da aka cimma tsakanin sassan dake da hannu a gwamnatin Zimbabwe ana fatan ɗorewar gwamnatin akan mulki

https://p.dw.com/p/LCX3
Shugaba Mugabe da Piraminista TsivangiraiHoto: picture alliance/dpa

Ba'a daɗe ba da ji daga bakin shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe cewar gwamnatin haɗin gambiza da aka kafa a ƙasar ba zata yi ƙarko ba. Kuma ko da yake har yau ana ci gaba da fama da gwagwarmayar riƙe madafun mulki a ƙasar ta Zimbabwe, amma fa a ɗaya ɓangaren akwai kyakkyawan fata game da ɗorewar gwamnatin.

Shugaba Robert Mugabe da abokin gabarsa P/M Morgan Tsivangirai sun ɗan nuna sassauci bisa manufa. Bayan watanni da dama na famar kai ruwa rana an warware wasu batutuwa waɗanda ke ba da ƙwarin guiwa game da ɗorewar gwamnatin haɗin gambizar ƙasar Zimbabwe. Dukkan sassan biyu sun amince da jami'ai da dama da za a naɗa domin bitar manufofin gyara ga dokar zaɓe da 'yancin 'yan jarida da kuma haƙƙin ɗan-Adam a ƙasar. Manazarta sun bayyana ƙwarin guiwarsu game da wannan ci gaba. Ko da yake a ganinsu har yau da sauran rina a kaba. An saurara daga Barnabas Thondlana, manazarcin al'amuran siyasa yana mai bayanin cewar:

"Abin da muke buƙata shi ne a ƙarfafa matsayin kafofi da kuma jami'an da aka naɗa. Ana dai iya maye gurbin mutane da wasu dabam, amma ita kanta kafar za a wayi gari tana ci gaba da fama da matsaloli."

A dai halin da ake ciki yanzun tilas ne a jira a ga yadda al'amura zasu kasance dangane da sanarwar da kakakin gwamnati ya bayar a game da wannan ci gaba. An dai shirya wata sabuwar ganawa tsakanin Mugabe da Tsivangirai, inda zasu tattauna ainihin muhimman matsalolin dake akwai a game da naɗin shugaban babban bankin ƙasar da kuma alƙalin-alƙalanta. Kazalika akwai maganar tabbatar da gwamnonin jiha. Mai yiwuwa a fuskanci mahawara mai tsananin gaske a Harare, fadar mulkin ƙasar ta Zimbabwe. A nasa ɓangaren dai P/M Tsivangirai yayi kira ga dukkan sassan da lamarin ya shafa da su nuna halin sanin ya kamata domin kyautata makomar ƙasar.

Jahresrückblick 2009 Flash-Galerie Simbabwe Tsvangirai Mugabe Koalition
Piraministan Zimbabwe Morgan TsvangiraiHoto: AP

"Muna fatan shawo kan kowace matsala a wawware akan wata manufa ta haɗin kai. Idan har mun haƙiƙance cewar matakan takunkumin na ƙasa da ƙasa na gurgunta al'amuran Zimbabwe to kuwa wajibi ne mu yi haɗin kai don ganin lalle an ɗage wannan takunkumi."

A misalin shekara ɗaya da ta wuce ne sassan biyu suka cimma daidaituwa akan kafa wata gwamnati ta haɗin gambiza bayan famar kai ruwa ranar da aka yi dangane da zaɓen ƙasar. Tun daga wancan lokaci aka fara samun kyakkyawan ci gaba a Zimbabwe, ko da yake ba zata yiwu a samu canjin al'amura a cikin ƙiftawa da Bisimilla ba, amma duk haka jama'a sun samu 'yar sararawa idan an kwatanta da yadda al'amura suka kasance a ƙasar gabanin shekara ɗaya da ta wuce. Maƙobciyar ƙasa ta Afirka ta Kudu tana taka muhimmiyar rawa a ƙoƙarin ɗinke ɓarakar dake akwai a Zimbabwe, kuma shugaba Jacob Zuma na marhabin da irin ci gaban da aka samu a matsayin matakin farko akan wata nagartacciyar hanyar da zata kai ga tudun dafawa.

"Al'amari ne dake da sarƙaƙiyar gaske. Mun tattauna da ƙawayenmu a Zimbabe, sun kuma nuna shirinsu na na tabbatar da aikin gwamnatin da aka naɗa. A saboda haka wajibi ne mu ba su goyan baya."

A yanzun dai ba abin da za a yi illa a saurara a ga ire-iren abubuwan da zasu biyo baya.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal