1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

.: HALIN DA AKE CIKI BAYAN KAMMALA ZABE A IRAQI.

January 31, 2005

mutanen kasar iraqi a layin jefa kuria a lokacin zaben gama gari

https://p.dw.com/p/BvdO
Hoto: AP

A yanzu haka dai ta faru ta kare wai anyiwa mai dami daya sata. Bayan wani dogon lokaci da aka dauka game da ranar daya dace a gudanar da zaben gama gari a iraqi,a jiya lahadi ne wadanda suka cancanci yin wan nan zabe a kasar ta Iraqi da kuma wasu kasashe na duniya suka kada kuriun nasu a wan nan zabe mai dimbin tarihi.

Rahotanni da suka iso mana sun shaidar da cewa kashi kusan sittin ne na mutanen da sukayi rijista da hukumar zaben suka fito don kada kuriun nasu a wan nan zabe dake a matsayin irin sa na farko a tsawon shekaru hamsin da suka gabata.

Rahotannin sun ci gaba da nuni da cewa duk da kwararan matakan tsaro da aka dauka a fadin kasar an fuskanci tashe tashen hankula da kuma rikice rikice a kasar ta iraqi.

A misali bama bamai sun tashi a lokacin gudanar da wan nan zabe a Birnin Bagadaza da kuma Garin Mosul da kuma Basra,wanda hakan byayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan talatin da shida banda wasu kuma da yawa da suka jikkata.

A dai gaba ki daya jamian tsaron na Iraqi tare da hadin gwiwar sojojin Amurka sun cafke mutane a kalla 200 da suke zargi sun nemi tayar da zaune tsaye a lokacin wan nan zabe na jiya lahadi.

Rahotanni dai a yanzu haka sun shaidar da cewa tuni akayi nisa wajen fara kidayar kuriun da aka kada a zaben na jiya,kuma da alama sakamakon zaben baki daya ka iya fitowa nan da kwanaki a kalla goma masu zuwa.

Babban dai abin da ka iya kawo cikas game da wan nan zabe shine na yadda yan darikar sunni a kasar suka kauracewa wan nan zabe na jiya lahadin.

Duk da cewa wasu daga cikin shugabannin kasashen duniya na bayyana fatansu na samun dorewar zaman lafiya a kasar ta iraqi a hannu daya kuma da yawa daga cikin masu nazarin siyasar kasa da kasa na tunanin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba game da dorewar mulkin dimokradiyya a kasar ta iraqi.

Wan nan dai raayi na masu nazarin siyasar ya samo asali ne game da kauracewa zaben da yan darikar sunni sukayi a waje daya kuma da yawaitar tashe tashen bama bamai a wasu yankunan kasar na iraqi.

A waje daya kuma shugaba Bush na Amurka na ganin cewa wan nan zabe na jiya a yanzu haka na a matsayin wata kafa ne na tabbatuwar mulkin dimokradiyya a kasar ta iraqi. Shi kuwa sakataren mdd Kofi anan cewa yayi majalisar ta dd zata taimakawa kasar ta iraqi a nan gaba wajen tsára kundin mulkin ta.

A daya hannun kuma faraministan Biritaniya Tony Blair shima bayani yayi da cewa wan nan zabe kafa ce da yan iraqi zasu samu tabbataccen yancin su na tafiyar da harkokin kasar su da kansu.

A daya barin kuma shugaba Vladimir Putin na Russia wanda na daya daga cikin shugabannin kasashen duniya da suka soki lamirin yakin kasar iraqi da amurka ta Jagoranta, bayyana fatan sa yayi a yau litinin da cewa a yanzu haka kasar ta iraqi ta hau turba da zata kaita tudun mun tsira.

A daya wajen kuma a yanzu haka ma,aikatar harkokin tsaron kasar Biritaniya na nan naci gaba da binciken musabbabin hatsarin jirgin saman nan kirar Hercules 130 da yayi hatsari jiya a arewa maso yammacin Birnin Bagadaza.

Hatsarin wan nan jirgi dai dake hanyar sa izuwa Birnin Bagadaza daga garin Balad yayi sanadiyyar ajalin sojojin kasar ta Biritaniya guda tara.

Ibrahim Sani.