1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki dangane da cutar Murar Aladu.

April 29, 2009

Matakan kariya da riga kafi tsakanin gwamnatocin ƙasashen duniya dangane da ɓarkewar cutar murar Aladu

https://p.dw.com/p/HgVU
Gonar AladuHoto: AP

Hankullan ƙasashen duniya na cigaba da kaɗuwa adangane da yaɗuwar sabuwar annobar nan ta murar aladu da ta samo tushe daga ƙasar Mexiko.

Ƙasashe dabam dabam na duniya na cigaba da ɗaukar matakan riga kafi.

Wannan cuta ta murar Aladu data samo tushe daga Mexico tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 150, kana wasu dubu biyu suna cigaba da jinya, kuma ta na cigaba da bazuwa babu ƙaƙƙautawa.

Saboda haka ne ƙasashe dabam dabam na duniya suka fara ɗaukar matakai da zummar shawo ta.

Wannan matakai sun haɗa da ƙarfafa binciken kiwon lafiya a filayen saukar jiragen sama, mussaman ga fasenjojin da suka fito daga yankin Latin Amirka.

Rahotanni daga kasar Mexico dai na nuni dacewar an samu karin wadanda suka rasa rayukansu kamar yadda mataimakin Babban Directa na hukumar lafiya ta duniya Keiji Fukuda ya bayyana...

Keiji Fukuda, WHO
Keiji FukudaHoto: AP

Yace "Mun samu karin mutane 26 daga jihohi daban daban guda huɗu da suka kamu da wannan cuta, kuma bakwai daga cikin su sun riga mu gidan gaskiya, kuma dukkanninsi a kasar Mexico ne"

A ɗaya hannun wasu ƙasashe sun dakatar da shigo da naman aladu da dangoginsa, duk kuwa da cewar ƙwararrun likitoci sun tabbatar da cewar, ba ta cin naman alade ake kamuwa da cutar ba.

Yanzu haka dai cuɗanya tsakanin alummomi da wannan cuta ta ɓarke ya zamanto abun damuwa kasancewar ba lallai ne aga alamun cutar a kwanakin farkon kamuwa da ita ba, kamar dai yadda wannan matashin na kasar New Zealan ya shaidar....

" Murar aladu ya zamanto babban damuwa, domin baka san wake dauke da cutar ba tunda ba ganin alamunsa za a yi nan take ba"

A nahiyar Afrika, duk da cewar cutar ba ta ɓulla ba,tuni ƙasashe sun fara shiga shirin kota kwana.

Ƙasashen da suka riga suka ɗauki matakai, ya zuwa wannan lokaci sun haɗa da Maroko, Masar, Ghana, Niger, Afirka ta Kudu Zambia da Mozambik.

Hukumomin Morroko alal misali sun yanke shawara tsaurara bincike lafiya a tashoshin jiragen ruwa filayen saukar jiragen sama da iyakokin ƙasar.

A nasu ɓangaren hukumomin filin saukar jiragen sama birnin Alƙahira, sun daɗa sa ido tare da yin binciken ƙwaƙƙwap ga dukkan fasenjojin da suka fito daga Mexiko.

Ƙasar Ghana a nata gefe, ta haramta shigo da naman aladu kwata kwata, tare da kafa komiti na mussamman da aka ɗorawa naunin bin diddigin halin da ake ciki, a game da cutar murar aladu.

Wannan matakai na riga kafi, sun yi kama da wanda hukumomin Afirka ta Kudu da Zambiya suka ɗauka.

Saidai daga dukkan ƙasashen Afirka, Mozambik ta fi ɗaukar matakai masu tsauri, domin fadar gwamnatin Maputu, ta kafa abunda ta raɗawa suna dokar ta ɓaci a akan wannan cuta.

Mexiko Schweinegrippe Passanten mit Mundschutz
Al'ummar MexicoHoto: picture alliance / landov

Daraktan hukumar kiwan lafiya ta ƙasa Leonardo Chavane ya tabbatar da cewar sun lunka bincike a kan duk mutanen dake fama da rashin lafiya, sannan sunyi tanadi na mussamman, a tashoshin jiragen ruwa.

To sai a yau an tabbatar da mutum guda daga rasa ransa daga kamuwa da wannan cuta a Amurka.

Kafin hakan dai kasar Mexiko ce kadai aka yi asaran rayukan mutane fiye da 150, bayan sama da 2,000 da suke fama da jinya.Jamus da Australia dai dai sune kasashen turai na baya bayan nan da cutar ta shafa.

Kawo yanzu dai hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar dacewar bata da allurar rigafin kamuwa da cutar murar aladun, sai dai Amurka tayi alkawarrin samar da guda cikin watan Mayu mai kamawa.


Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Umaru Aliyu