1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki game da rikicin Nukiliyar Iran

Ibrahim SaniDecember 6, 2007
https://p.dw.com/p/CYNA

Ƙasar Sin ta ce tana nan akan bakanta na a ci gaba da tattaunawar sulhu game da rikicin nukiliyar Iran, a maimakon amfani da ƙarfin soji. Mahukuntan na Beijin sun ce suna nan su na ci gaba da nazarin rahoton hukumar Leken asirin Amirka dangane da shirin Nukiliyar na Iran. Rahoton dai ya yi nu ni da cewa Iran ta dakatar da shirinta na mallakar makamin Atom ne daga tun shekara ta 2003. Sabon rahoton a yanzu haka ya kasance babbar barazana ga shirin shugaba Bush na ganin an ƙaƙabawa Iran takunkumi. Tuni dai shugaba Mahmud Ahmadinejad ya yaba da wannan rahoto, da cewa babban ci gaba ne game da cacar baka dake, a tsakanin Iran da ƙasashen yamma.