1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA KASAR IRAQI KE CIKI A YAU.

July 7, 2004

HOTON IYAD ALAWI A TSAKIYA TARE DA PAUL BREMER DA KUMA BABBAN JOJIN KASAR IRAQI.

https://p.dw.com/p/BviM
Hoto: AP

Har yanzu dai bata sake zane ba game da tabarbarewar harkokin tsaro a kasar iraqi duk kuwa da mikawa yan kasar harkokin mulki da dakarun mamaye bisa jagorancin Amurka sukayi makonni kusan biyu da suka gabata.

A misali a safiyar laraba an fuskanci wata arangama mai munin gaske a tsakanin yan fadan sari ka noke da jamian tsaro na kasar ta iraqi a hannu daya kuma da dakarun sojin Amurka.

Rahotanni dai sun nunar da cewa yan fadan sari ka noken sun bude wuta kann mai uwa da wabin ne kann wasu sojin tsaro na musanman dake kasar ta iraqi.

Hakan yayi sanadiyyar mutuwar jamian tsaro biyu na kasar ta iraqi a hannu daya kuma da jiwa wasu guda goma raunuka iri daban daban.

Jim kadan bayan aukuwar wan nan al,amari ne dakarun sojin Amurka da wani karamin jirgin yaki suka bayyana a gurin da abin ya faru domin kawo dauki tare da mayar da martani ga yan fadan sari ka noken.

Bayanai dai daga kasar ta iraqi sun shaidar da cewa anyi musayar wuta mai tsananin gaske a tsakanin yan fadan sari ka noken da dakarun sojin Amurka a dai dai gurin da wan nan al,amari ya faru.

Wan nan dai al,amari a cewar bayanan da suka iso mana ya faru ne jim kadan bayan gwamnatin rikon kwaryar ta bada sanarwar kafa dokar ta baci a wasu yankuna na kasar bisa hujjar inganta harkokin tsaro a fadin kasar baki daya.

A cikin wani taron manema labarai da jamian gwamnatin suka gudanar a yau sun bayyana cewa daukar wadan nan matakai ya zama dole bisa irin halin rashin tsaro dake ci gaba da addabar kasar ta iraqi.

A cikin wan nan sabuwar doka da Faraminista Iyad Alawi ya rattaba hannun amincewa ta tabbatar da bawa gwamnatin sa cikakken ikon saka dokar ta baci a duk guraren da suke ganin yin hakan ya dace ya zuwa wani dan lokaci.

A wata sabuwa kuma bayanai daga kasar ta iraqi sun nunar da cewa an fuskanci tashin wasu bama bamai a kusa da ofishi da kuma gidan faraminista Iyad Alawi,to amma a lokacin da wan nan al,amari ya faru baya cikin gidan nasa ballantana ofis din.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya jikkata ko kuma ya rasa ransa sakamakon tashin wadan nan bama bamai.

Daga dai tun lokacin da aka mika mulki ga yan kasa ya zuwa yanzu babban abin da ke ciwa gwamnatin ta Iyad Alawi tuwo a kwarya shine rashin kyakkyawan tsaro a kasar ta iraqi.

Ba a da bayan wan nan kuwa sai batun samar da abubuwan more rayuwa da kuma farfado da tattalin arzikin kasar da yake neman durkushewa.

Duka dai wadan nan mtsaloli a cewar masu sharhin abin da kaje yazo na gabas ta tsakiya za a iya shawo kansu ne kawai matukar an samu kyakkyawan tsaro a fadin kasar ta iraqi baki daya a hannu daya kuma da samun goyon bayan da ake bukata daga yan kasar ya zuwa gwamnatin rikon kwarya da Iyad Alawi kewa jagoranci a halin yanzu.

Ibrahim Sani.