1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA KASAR IRAQI KE CIKI.

Maryam L.Dalhatu.September 20, 2004

A yayin da zaben shugaban kasa ke dada karatowa a iraqi,babu wani canji dangane da tashe tashen hankula da ake fuskanta a kasar.

https://p.dw.com/p/BvgL
PRIME MINISTAN IRAQ,IYAD ALLAWI.
PRIME MINISTAN IRAQ,IYAD ALLAWI.Hoto: AP

Rahotanni na dada nuni da yadda ake cigaba da fuskantar tashe tashen hankula a kasar iraqi,inda ko a yau dinnan sai da Muqtadr Sadr yayi kira ga yan tawayen da suka yi garkuwa da wasu yan iraqin goma sha takwas da su sake su.

Wadannan yan tawaye sun bada waadin saoi arbain da takwas ga gwamnatin kasar data sako dan shian nan Hazem Alaaraji dake tsare,ko kuma su halaka wadannan mutane goma sha takwas.

Can kuma a fallujah jiragen yakin amurka ne keta sakin boma bomai a inda suke zargin nan ne maboyar yan yakin sari ka noke dake kasar.

Bisa wannan ne kuma maaikatar kula da lafiya ta iraqi ta fidda rahoton dake bayanin cewa mutane bakwai ne suka rasa rayukansu wasu goma sha hudu kuma suka raunana daga jiya lahadi zuwa safiyar yau litinin.

A yammacin jiyan kuwa wasu yan bindiga dadi ne suka harbe wani babban malami dan sunna a bagadaza,mai suna Sheik Hazem Alzeidi.tare kuma da yin garkuwa da masu tsaron lafiyar sa.

Sai dai bayanai a yau sun tabbatar da cewa an saki wadannan masu tsaron lafiyar nasa biyu.yan shia da yan sunna a iraqi musamman ma a garin sadr suna fuskantar hare hare a wuraren bautarsu,wanda kuma suke nuna bacin ransu ga yadda yan sandan kasar keyin biris da alamarin.

A yau ne kuma waadin da yan tawayen da suka yi garkuwa da amurkawa biyu da dan britaniya daya suka bawa kasar amurka ke cika inda suka bukaci amurkan da ta saki matan kasar iraqi dake tsare a hannun ta,ko kuma su halaka wadannan mutane uku.

Sai dai jamian tsaron amurkan sun bayyana cewa mata biyu ne a tsare wadanda kuma suna cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar Saddam Hussein,bisa niyyar sa ta kera makaman kare dangi.

Prime ministan iraqi mai rikon kwarya Iyad Allawi da a yanzu yake britaniya ya dauki alkawarin daukar duk wani mataki na ganin yan tawayen sun saki wadannan mutane uku.

Duk kuwa da cewa shi kansa sau hudu yana sha da kyar a hare haren da yake fuskanta tun bayan daya karbi mulkin kasar.

Haka kuma Iyad Allawi a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar britaniyan Toni Blair ya cigaba da cewa babu wani abu da zai hana gudanar da zaben kasar a watan janairu mai zuwa kamar yadda aka shirya,inda yayi kira ga majalisar dinkin duniya data bada agajin tabbatar da hakan.

Sai dai a yayin da yake nasa shiri su kuma can a kasar iraqin suna cigaba da fuskantar tashin hankali,inda ake cigaba da rasa rayuka, kuma ake cigaba da yin garkuwa da mutane.

Yan sanda a garin kirkuk sun bada rahoton batan wasu direbobi yan kasar turkiyya su goma sha biyu,wadanda ake ta nema tun daga jiya lahadi zuwa yau litinin,ana dai zargin cewa wata kungiyar yan tawayen ce ta capkesu,idan ma ba halaka su akayi ba.

Ire iren wadannan rikice rikice ake cigaba da wayar gari dasu a kowacce rana a kasar iraqi,domin kuwa bincike ya tabbatar da cewa a watannan kawai sama da mutane dari hudu ne suka rasa rayukansu.