1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da makiyaya ke ciki ya ɗauki hankalin jaridun Jamus

December 13, 2009

An samu ɓillar wata ƙungiya ta haɗin guiwar adawa da shugaba Joseph Kabila na ƙasar Kongo

https://p.dw.com/p/L1UM
Shugaban ƙasar Kongo Joseph KabilaHoto: AP Photo

A wannan makon dai matsalar ɗimamar yanayin duniya ita ce ta fi ɗaukar hankalin jaridun Jamus. Amma da farko zamu fara da wani sabon rikicin da ya kunno kai a janhuriyar demoƙraɗiyar Kongo, inda aka samu wata haɗin guiwa tsakanin magoya bayan Bemba da dakarun marigayi Mobutu dake yaƙar gwamnatin Kabila a yankin arewa-maso yammacin ƙasar. A lokacin da take ba da rahoto akan haka jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Wata ƙungiyar adawa ta haɗin guiwa tsakanin dukkanin ƙungiyoyin dake ƙyamar mulkin shugaba Joseph Kabila su ne kuma ke da alhakin hare-hare da dama da aka riƙa kaiwa a lardin Equateur dake arewa-maso yammacin Kongo. Bisa ta bakin wani mai magana da yawun ƙungiyar ya ce a yanzun sun gabatar da wani mataki ne na farko akan hanyarsu ta yin kaca-kaca da gwamnatin mamaye dake mulki a Kinshasa. Lamarin yayi tsamari, inda a farkon wannan mako shugaba Kabila ya ce zai tura dakarun soja 600 zuwa Mbadanka, shekwatar lardin. Su ma sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya na kan hanyansu zuwa yankin".

Makiyaya sun yi ɗaruruwan shekaru suna jure fari a nahiyar Afirka, amma a yanzu lamarin na nema ya ta'azzara sakamakon canje-canjen yanayin da ake samu a sassa daban-daban na duniya. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Süddeutsche Zeitung ci gaba tayi da cewar:

Kenia Dürre bei Athi tote Kühe
Makiyaya na fama da ƙarancin wuraren kiwo sakamakon ɗimamar yanayin duniyaHoto: picture alliance / dpa

"A ƙasashe irinsu Kenya da Uganda mutanen da lamarin ya shafa ba su da faɗa a ji a harkoki na siyasa, kuma galibi masu fama da raɗadin kan koka a game da cewar ba a tuntuɓarsu domin jin ta bakinsu a duk lokacin da ake neman bakin zaren warware matsalolin dake addabarsu. Hakan ya sanya suke ɗariɗari da gwamnati. A zamanin baya makiyayan sun sha fafatawa ne da 'yan mulkin mallaka amma a yau suna fama ne da mahukunta na cikin gida, waɗanda suka karɓi madafun iko bayan samun 'yancin kai".

Bisa ga ra'ayin jaridar ta Süddeutsche Zeitung dai ɗimamar yanayin duniyar na ɗaya daga cikin ummal'aba'isin yaƙe-yaƙen da ake fuskanta a Afirka, saboda ta haifar da ƙarancin ruwa da wuraren kiwo da ma ƙarancin sauran albarkatu.

Shugaban babban bankin Nigeria na taka muhimmiyar rawa a fafutukar murƙushe ɗabi'ar nan ta cin hanci da tayi wa 'yan Nijeriya katutu in ji jaridar kasuwanci ta Handelsblatt. Jaridar ta ƙara da cewar:

"Duk da namijin ƙoƙari da shugaban babban bankin Nijeriya Sanusi Lamiɗo yayi na sake maido wa bankin martabarsa da ɗaga matsayin jarinsa, amma kuma har yau da sauran rina a kaba, saboda akwai basussuka da dama na bankin da aka karɓa ba akan gaskiya ba saboda rashin nagartar tsarin ba da rancen kuɗin. A yanzu sai a sa ido kan sabuwar alƙiblar da shugaban babban bankin Nijeriyar ya fuskanta, ko Ya-Allah zai samu nasara bisa manufa".

Masu sauraro ƙarshen rahotannin jaridun na Jamus akan al'amuran Afirka ke nan. Rahmatu gare-ki.