1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da yan jarida ke ciki azirin Gaza

February 5, 2007

Yan jarida nacigaba da fuskantar barazanar a tafiyar da yyukansu

https://p.dw.com/p/BtwN
Zirin Gaza
Zirin GazaHoto: AP

Sakamakon rigingimun cikin gida dake cigaba da gudana tsakanin yan kungiyar fatah da Hamas na yankin palasdinawa,wanda kuma ya jefa alummomin yankin musamman wadanda ke zirin gaza cikin halin kakanikayi na rayuwa,Yan jarida na kafofin yada labarun ketare suma nacigaba da fuskantar barazar tafiyar da ayyukansu.gurnani kenan daga irin wannan arangama dake cigaba da gudana tsakanin yan Hamas da abokan mahayyarsu na kungiyar Fatah a zirin Gaza,kuma a hakan ne zaka ga motocin kafafan yada labarai dauke da rubutun kafar yada labarai da suke wakilta ke gudanar da ayyukansu cikin wannan hadari.

A ofishin gidan talabijin na Al Arabiyya,inda wakilan kafar yada labarun ke aikewa da rahotannin halin da ake ciki,suma baa barsu baya ba adangane da barazanar da suke fama dasu daga wadanda kan bugo musu waya.Wani wanda ya shirya wani rahoto dangane da premier Ismail Haniya na yankin palasdinwa daga yankin Islam Abdelkarim,ya bayyana wayan tangaraho daya samu daga wajen wani dabai fadi sunansa ba

“Yace bayan wannan labari ne muka samu wayoyin tangaraho daga mutane daban daban da basu fadi sunansu ba,inda suke mana gargadi.Sakamakon hakane muka zartar ta kauracewa ofishimmu,tare da gargadi wa sauran yan jarida cewa su kasance a gida,domin bamu san abunda zai iya biyo baya ba”.

Bayan hakane muka fuskanci yar matsala.Domin baa jima ba wasu ababai masu nasaba da boma bomai suka tarwatse a kofar ofishimmu,wanda ya haddasa fashewan kokofimmu da da tagogi ,kuma bangaren ginin ma ya rushe.Inda komai dake ilahirin wannan ginin ke bukatar gyara na gaggawa kafin a fara tafiyar da aiki.Sakamakon hakane dukkan wakilai da sauran maaikata basu koma bakin aiki ba,inda suka cigaba da kasancewa a gidajensu.

Akan hakane Islam Abdelkarim ya kara dacewa….

“Mu dai mun gabatar da rahoto ne akan hirar da mukayi da wadanda basu da hannu a wannan rikici na hamas dayan fatah,kuma ahalin yanzu bazamu iya cigaba da gudanar da ayyukanmmu ba ,tunda har yanzu akwai sabani tsakanin gwamnatin hamas da kafar yada labarai ta Alarabiyya”.

Wannan rikici dai bawai azirin gaza kadai yakewa yan jarida barazana wa ayyukansu na farautar labarai ba,amma har ma a kasar Jordan dake makwabtaka,rayuwa na cigaba da kasance abu mawuyaci wa manema labaran.Maher Shalabi dai shugaban wani kamfanin dillancin labaru ne dake birnin Ramalla..

“Yace a ranar 12 ga watan wannan shekara ne ,da misalin karfe 11 na dare ,muna cikin gida alokacin ma inada baki,sai mukaji harbin bindiga,kuma kusa da gidan,nayi tunanin cewa dakarun Izraela ne suka biyo wani,sai nayi kokaerin fita daga gina amma yaro na mai shekaru 8 da haihuwa ya kama yace kada in fita “

Irin wadannan hare ren dai basa hana mu gudanar da ayyukanmu na daukan labarai,muna yi duk da wannan barazana da muke fuskanta a kullum.