1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

.: HALIN DAKE FARUWA A IRAQI.

May 21, 2004

WAN NAN HOTON KUTUN DA AKE TUHUMAR SOJOJIN AMURKA NE DA SUKA TAFKA MUMMUNAN AIKI A GIDAN YARIN ABU GHRAIB A IRAQI.

https://p.dw.com/p/BvjP
Hoto: AP

Sakamakon matsi da kuma suka da dakarun sojin Amurka keci gaba da fuskanta a iraqi game da take hakkokin wasu fursunoni a gidan yarin Abu ghraib bisa hakan a karshen makon daya gabata ne dakarun sojin na Amurka suka sako wasu daruruwan fursunonin dake daurte a gidan yarin na Abu Ghraib.

Rahotanni daga kasar sun rawaito cewa bus bus kusan guda goma sha uku ne aka gansu dauke da fursunonin daga gidan yarin na Abu Ghraib izuwa cikin birnin Bagazada.

A wata sabuwa kuma a dai dai lokacin da wan nan abu ya faru a kuma lokacin ne jaridar Wshinton Post ta Amurka ta buga wasu sabbin bayanai na ire iren abubuwan dake faruwa a gidan yarin na Abu Ghraib.

Jaridar ta Washinton Post ta tabbatar da cewa daga cikin bayanan da suka iso mana sun nunar a fili karara cewa wasu batagarin sojin na Amurka sun gudanar da halayyar jaki ta duka kann fursunoni daurarrau dake gidan yarin na Abu Ghraib. Bayan nan kuma jaridar ta Washinton Post taci gaba da cewa sojojin sun kuma takurawa wasu daurarrrun shan giya da kuma cin naman alade,wanda kowa ya san Addinin musulunci dada dama daga cikin daurarrun ya naha wadan nan abubuwa guda biyu.

A waje daya kuma Jaridar ta Washinton Post tayi karin haske da cewa babu ko ja wasu dakarun sojin na Amurka sun yiwa wasu fursunonin mummunan fyade a cikin gidan yarin na Abu ghraib.

Jaridar ta tabbatar da cewa sabbin hotunan dake nuni da wadan nan abubuwan kunya da sojojin suka tafka an same su ne ta hannun kwamitin sojin bincike da aka kafa bisa hujjar bin kadin gaskiyar wan nan mummunan aiki da wasu sojojin Amurka suka tafka a can baya.

A waje daya kuma a jiya alhamis sojojin Amurka suka kaddamar da bincike na kwakwaf a cikin gidan daya daga cikin mambobin zartarwa na gwamnatin rikon kwarya wato Ahmed Chalabi da nufin awon gaba dashi don amsa wasu tambayoyi.

Kafin dai wan nan mamaye Ahmed Chalabi ya kasance daya daga cikin na hannun daman kasar ta Amurka daya fito daga iraqi,hasalima ya kasance a sahun gaba da Amurka ke aiki dashi kafada da kafada wajen sukar lamirin Gwamnatin Saddan Hussain.

A cikin wani taron manema labarai da Ahmed Chalabi ya gudanar jim kadan bayan wan nan mamaye da aka kai gidan sa ya tabbatarwa yan jaridu cewa a yanzu ya dawo daga rakiyar Amurka a don haka sojojin su fice su bar musu kasa. Yin hakan daga bangaren dakarun sojin na Amurka iji Chalabi shine zai taimaka wajen samun wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a fadin kasar baki daya.

A wata sabuwar kuwa rahotanni daga gari8n na Janaf sunyi nuni da cewa ana nan anaci gaba da arangama a tsakanin dakarun sojin na Amurka da kuma magoya bayan Moqtadar Sadr a can garin Najaf.

Koda a yau juma,a bayanai sun rawaito cewa an gani hayaki ya turnuke sararin samaniyar birnin sakamakon irin harbe harben gurneti dake wanzuwa a tsakanin bangarorin biyu.

A lokacin hudubar yau juma,a Moqtadar Sadr ya tabbatar da cewa arangama a tsakanin magoya bayan sa da dakarun sojin na Amurka yanzu ma aka fara matukar dai basu fice sun bar musu kasa ba.

Shugaban na Shi,awa ya nunar da cewa daya ja da baya game da yakar sojin na Amurka gwamma ya mutu a matsayin mai jihadi daya ke fafutikar nemarwa yan kasar sa yanci daga hannun dakarun sojojin mamayen.

IBRAHIM SANI