1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN RAYUWA A KASAR AFRIKA TA KUDU.

Maryam L.Dalhatu.August 20, 2004
https://p.dw.com/p/Bvh8

Thabiso Mahowa,na daya daga cikin yan kasar afrika ta kudu,wadanda ke zaune a cikin wani irin hali mawuyaci.a sabili da rashin tsabtataccen muhalli baya ga rashin ruwan sha,da hanyoyi wadanda ke sanyawa a kira gida gida ne.

A yanzu haka babban birnin dake hada hadsar cinikayya a kasar johannesburg yanzu ya farka daga barci na kalubalantar rayuwa tun bayan kawar da gwamnatin nuna wariyar jinsin fata a tsakanin bakake yan asalin kasar da fararen fatu wadanda sukayi kakagida.

Wannan birni a halin yanzu ya fara daukar matakai,na gine ginen sabbin matsugunai,maimakon wadanda a baya amfani dasu ya kasance a cikin halin haulai.

Kamar yadda kakakin gwamnatin wannan birni yace an dauki wannan mataki ne wanda cikin shekaru uku masu zuwa ake fatan kwalliya zata biya kudin sabulu.

Sanin kowa ne arewacin birnin na johannesburg wanda ke da cinkoso na alumma a yanzu zai zama birni kamar kowane birni a cikin kasar.

Mahowa,mai shekaru talatin da uku da haihuwa ta kwashe sama da shekaru hudu tana zaune a wani kuntataccen daki,tare da mijinta da kuma dansu dan wata goma sha daya.

Ta tabbatar da cewa a yanzu,gwamnati ta farka daga barcin daya kwashweta,na shekaru da dama da suka shude musamman dan bayar da tallafi na inganta kasa da inganta rayuwar talakawan kasar wadanda basu da abin goro a hannu.

Tace babban abin takaici idan tayi waiwaye wanda hausawa kance adon tafiya,shine lokacin sanyi wanda da ita da danta sukan fada wani irin hali mawuyaci.

Mahowa wacce a lokuta da dama,takan fada cikin birnin na johannesburg domin yin aiki a gidajen masu hannu da shuni domin ta sami abin da zata kai bakin salati.tace wani abin takaicin kuma,a kowanne lokaci mazauna wannan yanki,kann kasance a cikin halin zaman dar dar.musamman idan gobara ta tashi wanda nan take take kashe wanda take kashewa a sabili da zaman cikin gidajen kara.

Tace ko da kuwa,anyi kiran masu kashe gobara yan kwana kwana sukanyi togaciya da cewa babu hanyoyin da zasu isa don kashe wannan gobara,wanda wannan tsaiko kann haifar da mutuwar alumma da dama kama daga kananan yara zuwa manyan su.

Kamar yadda Modingwane,daya daga cikin jamian gwamnatin wannan birni yace wannan na daya daga cikin hanyoyin da zaa dauka na magance wannan matsala ta mayar da wannan sansanin talakawa ya zama kananan gidaje na zamani a cikin shekaru uku kamar yadda gwamnati ta alkawarta.

Yace ya zama wajibi a samar da hanyoyi,domin cimma wannan buri da aka sanya a gaba baya ga ruwan sha da wutar lantarki,da tsabtace muhalli da makarantu da asibitoci da kuma filayen shakatawa.

To sai dai wata malama a jamiar Marie Huchzermeyer,masaniya a fannin tsare tsaren gine gine ta nuna shakku na cimma wannan manufa,tace da wuya a cikin shekara uku a kammala wadannan tsare tsare kamar yadda gwamnati ta fada a baya,ta dai tabbatar da cewa zaa iya cimma wannan nasara cikin shekara biyar masu zuwa idan har an yi hattara.

Shugaba Thabo Mbeki na afrika ta kudu a cigaba da rike madafan iko a karo na biyu a kasar ya lashi takobin kakkabe talauci da fatara da cutuka da suke addabar mazauna ire iren wadannan matsugunai.

A bisa wata kididdga dai ya nunar da cewa kasar ta afrika ta kudu nada kusan million biyu irin wadannan matsugunai,wadanda ke dauke da sama da million bakwai na mutane.

Ana kumna fatan kwalliya zata biya kudin sabulu wajen magance wannan matsala da gwamnatin tasa gaba.