1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rayuwa a liberia

Mansour BBNovember 6, 2003
https://p.dw.com/p/Bvnm

Magabatan kasar Liberia a yanzu sun dauki wani mataki na magance zaman kashe wando ga baragurbin wadanda suka fito fagen daga a lokacin yakin basasar kasar na sama da shekaru 14 .A kalla dai a kwai sama da wadannan mutane musamman matasa dubu 40 wadanda basu da aikinyi kuma sun dandana yaki a kasar ta Liberia .A bisa wannan halin ne gwamnatin rikon kwarya ta kasar ta dauki alwashin samar da aikinyi garesu domin kada nan gaba su sake fadawa wani irin tarko irin wannan .Za dai a fara wannan aikin ne a tsakiyar wannan Watan da muke ciki Za kuma a cimma wannan manufar ne bisa hadin guiwwa ta gwamnatin kasar da kungiyar yan rtawayen kasar ta LURD da kuma Model da kuma kungiyar Ecowas baya ga bankin Duniya da kuma kungiyar gamaiyar urai duka sun dauki nauyin bayar da tallafi domin tabbatar da shirin ya sami karbuwa Ga masu nazarin alamurran rayuwa kuwa sun tabbatar da cewa shirin zai dawo da martabar kasar tare da mantawa da yakin da aka gwabza na tsawon lokaci wanda ya haifar da kaura ga yan kasar wanda adadin su ya tasamma miliyan ukku da da rabi ..A Yakin na baya bayan nan a kalla mutane dubu 50 ne suka mutu baya ga fyade da aka dunga yiwa yan mata da manyansu a kasar a kokarin kwadayin mulkin kasar ta liberia .Tun daga shekara ta 1989 MDd ke kokarin ganin an shawo kann yakin basasar daya barke a kasar inda madugun yan tawayen wancan zamanin Chasrles Taylor ya dauki gabarar yaki da Gwamnatin kasar har sai da aka gudanar da zabe a kasar a shekara ta 1997 inda aka zabi Taylor ya zama shugaban kasar ,a yanzu dai Tsohon shugaban na Nigeria bisa gudun hijira bayan da yaki ya sake ballewa a kasar ta Liberia daga bisani ya sami matsin lamba daga kasashen Amurka da yammacin turai cewa mafita daya itace ta yafita daga kasar domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa .Har kawo yanzu kuwa sauran tsirarunmatasan dake cigavba da haifar da zaune tsaye basa cikin hayyacin su sabili da sun kasance yan kwaya ne ko kuma yan ganye a takaice .A dangane da haka ne dole gwamnatin kasar ta tashi tsaye domin wannan halin da matasan kasar ke ciki .Bayan da aka zanta da daya daga cikin kwamandojin yakin yan tawayen kuwa cewa yayi shi kam ya shiga aikin soji kenan domin acewarsa ya sami dabarun yaki .Shi dai annan yaro mai shekaru 22 yace batun zaman lafiya a gareshi a kasar ta liberia babu shi kuma babu dalilinsa .Shi kuwa wani Yaro wanda shima ya fafata a yakin na Liberia mai shekaru 9 yace a yanzu kann ya gane kurensa na yakar yan uwa batare da sanin hakikanin gaskiyar lamari ba .Tuni dai wasu daga cikin yan tawayen suka mika makamnsu ga gwamnati a yayin da wasu kke rike dasu da cewa Yaki yanzu aka fara shi matukar babu adalci a kasa .To sai dai wasu daga cikin kwamandojin yakin kann nemi kudade domin kwance damarar yaki wanda a hannu guda gwamnati da kungiyoyin mDd kann hana afkuwar hakan ..kamar yarda daya daga cikin maaikatan MDd a kasar mai suna Fatima tavce bayar da kudade bai zama abun tasiri ba sai dai samar da aikinyi ga jammaa wanda hakan ka iya haifar da zaman lafiya a kasar