1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rayuwar Yahudawan Habasha a Isra´ila.

Mohammad Nasiru AwalDecember 5, 2003
https://p.dw.com/p/BvnF
Wata da ake kira Nurit wadda tun tana yarinya ´yar shekara 5 da rabi aka kai ta Isra´ila ta ce abin da take iya tunawa a lokacin da suka isa wannan kasa shine wani dandano dabam na ´ya´yan itace, kana kuma wannan lokaci ne karon farko da ta taba ganin farar fata. Ita dai Nurit da iyalanta na daga cikin ´yan kasar Habasha da aka yi jigilar su daga wannan kasa zuwa Isra´ila saboda matsalolin yunwa, yakin basasa da kuma wariyar da ake nuna musu. A wancan lokaci gwamnatin Isra´ila ta kirkiro wani shiri da nufin samun saukin shigar da wadannan ´yan kaura daga Afirka cikin jama´a, to sai dai bisa ga dukkan alamu wannan shiri bai cimma manufar da aka sa gaba ba. Yanzu haka dai Nurit wadda ta cika shekaru 25 da haihuwa, ta zama cikakkiyar ´yar Isra´ila kuma tuni ta kammala karatun jami´a a kasar Amirka. Ta ce yanzu dai babu wani abin da take iya tunawa da Habasha. A halin da ake ciki akwai Yahudawa ´yan asalin kasar Habasha kimanin dubu 35 a cikin Isra´ila, to amma har yanzu da yawa daga cikinsu na fama da wahalhalu iri dabam dabam kamar na yare, bambamcin al´adu ga kuma matsalolin rashin aikin yi. Har yanzu dai da yawa daga cikin Yahudawan Habasha na zama ne a unguwanni talakawa marasa galihu, kana kuma ba su da ilimi kamar takwarorinsu Isra´ilawa, wato har yanzu suna daukar kansu a matsayin baki cikin Isra´ila.
Wata masaniya a fannin zamantakewar jama´a, Esther Herzog ta yi korafin cewa shirin gwamnati na tsugunar da Yahudawan Habashan ne musabbabin matsalar da wannan al´uma ke fuskanta. Domin lokacin da ´yan Habashan suka fara isa Isra´ila, an rarraba su da juna, an yi ta tsugunar da su a wasu unguwanni da ba su dace ba, sannan maimakon a bar yara a karkashin kulawar iyayensu, sai aka rika turasu makarantun kwana. A makarantun koyan sana´a kuma an warewa ´yan kaurar daga Habasha wasu fannoni ne dabam, wanda ko kadan bai taimaka ba. Wato maimakon wannan shiri ya hadesu da sauran jama´a sai ya kara mayar da su saniyar ware a cikin Isra´ila.
Misis Herzog ta ce tun da farko fari, in da an kyale Yahudawan Habashan sun warwatsu a ko-ina cikin Isra´ila kamar takwarorinsu Yahudawan Rasha, to da an samu saukin shigar da su cikin jama´a.