1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin siyasa a kasar Zimbabbwe

ibrahim saniJune 2, 2005

Al,amurra dai naci gaba da tabarbarewa a kasar Zimbabwe,kama dai daga siyasa da tattalin arziki da kuma zaman takewa

https://p.dw.com/p/BvbW
Hoto: AP

Da farko dai shugaba Robert Mugabe ya bukaci sabuwar majalisar dokokin kasar data fara zaman ta a ranar tara ga watan nan da muke ciki sabanin lokacin da aka tsara a can baya.

Kiran wannan zama na majalisar daka iya kasancewa na farko a tun bayan kammala zaben yan majalisun dokokin kasar,da alama bai samu karbuwa ba daga bangaren wasu yan majalisar dokokin kasar,musanmamma daga bangaren yan jamiyyar adawa ta MDC.

A cewar magatakarda na majalisar dokokin kasar a lokacin wannan zama ana bukatar a tattauna batun kudiri ne da jamiyyar Zanu ta Mugabe ta gabatar game da kirkiro babbar majalisar dokoki a kasar da in har ta kasance zata zama ta farko a tun lokacin da kasar ta samu yancin mulkin kai.

Rahotanni dai a yanzu haka na nuni da cewa majalisar zata gudanar da zaman nata ne a wani yanayi na matsi da yamutsi da kasar take fuskanta game da dagulewar harkokin siyasa da kuma koma bayan tattalin arziki.

Ba a da bayan wannan yanayi akwai kuma batun kin amincewa da sakamakon zaben yan majalisun dokokin kasar daya bawa jamiyyar ta Zanu nasara akan abokiyar karawar ta wato MDC ta shugaba Morgan Changirai.

A yayin da kuwa ake cikin wannan hali a daya hannun kuma kasar yanzu haka a shirye take ta fara karbar tallafin abinci daga hukumar kula da abinci ta mdd.

Wannan mataki dai ya biyo bayan wata ganawa ne da akayi a tsakanin shugaba Robertz Mugabe da kuma wani jamiin hukumar daya kai ziyarar aiki izuwa kasar.

A can baya dai gwamnatin ta Mugabe ta dauki matakin kin amincewa da karbar tallafin abincin duk kuwa da matsalar abincin da a kalla mutane miliyan hudu na kasar ke fama da ita.

Game kuwa da wannan mataki da shugaba mugaben ya dauka wanda ake hasashen cewa watakila ya canja daga baya Sakataren Mdd Kofi Anan ya shaidar da cewa wakilin sa na musanman a kasar Africa ta kudu wato Jemes Moris ya tabbatar masa da cewa gwamnatin ta Mugabe tayi amanna dari bisa dari da wannan tayi da aka gabatar musu.

Shugaba Mugabe dai da a yanzu keda shekaru 81 ya dora laifin matsalolin da kasar sa ke ciki ne akan kasar Biritaniya da tayi mudu mulkin mullaka.

A wata sabuwa kuma jamiin yan sanda na kasar ta Zimbabwe sun cafke wasu mutane a kalla dubu ashirin biyu da dari bakwai da talatin da biyar a wani kame da suka gudanar a cewar jaridar kasar mai suna Herald.

Mutanen wadanda ake zargi sun giggina guraren kwana a kusa da wasu manya manyan birane,kamen nasu ya samu suka mai yawan gaske daga bangarori da dama na kasar.

A misali hukumar kare hakkin bil adama ta Amnesty International tayi watsi da wannan mataki da cewa aiki ne na take hakkokin na bil adama kawai.

Haka itama jamiyyar adawa ta kasar wato MDC tayi Allah wadai da wannan mataki da cewa ka iya kara dagula al,amurra a kasar.

To amma a waje daya kuma jamian gwamnatin na Mugabe sunce sun gudanar da wannnan aikin ne don dasa aya game da kasuwannin bayan fage da gidaje da aka gigginawa ba bisa kaida ba.