1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin siyasa a lardin Ireland Ta Arewa bayan sanarwar ajiye makami ta kungiyar IRA

Mohammad Nasiru AwalJuly 29, 2005

Dole aiki ya biyo bayan sanarwa kawo karshen daukar makami da kungiyar IRA ta bayar.

https://p.dw.com/p/Bvak
IRA ta yi shailar kawo karshen gwagwarmaya da makami
IRA ta yi shailar kawo karshen gwagwarmaya da makamiHoto: AP

Yanzu dai maganar wanzar da zaman lafiya ake yi amma ba tsagaita wuta ba, domin an kawo karshen yakin sunkuru da daukan makamai da aka shafe shekaru 35 ana yi, inji sanarwar da kungiyar ´yan tawayen Ireland Ta Arewa wato IRA ta bayar. A hukumance yanzu an kawo karshen wani yakin basasa a Birtaniya da ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane dubu 3 da 600. Sanarwar ta yi kira ga dukkan ´ya´yan kungiyar IRA da su ajiye makamansu sannan tun daga yanzu su fara bin hanyoyin lumana don cimma manufofinsu na siyasa.

An yi maraba tare da nuna shakku ga sanarwar. Hatta shi kan shi FM Birtaniya Tony Blair da takwaran aikinsa na janhuriyar Ireland Bertie Ahern sun dan nuna shakku a martani da suka mayar. FM Ahern ya ce sanarwar ka iya zama wani ci-gaba na tarihi idan wani sahihin aiki ya biyo baya. Sannan shi kuma Blair cewa ya yi akalla yanzu ana da fatan kawo karshen wannan rikici.

Mutumin da ya fi nuna shakku shi ne Ian Paisley shugaban jam´iyar ´yan ra´ayin rikau ta Democratic Unionist. Paisley ba kawai rikakken mai adawa da kungiyar IRA da bangaren ta na siyasa ba ne wato Sinn Fein, a´a ya kasance babban mai fada a ji a takanin ´yan siyasar protestan na Ireland Ta Arewa musamman tun bayan zaben da ya gudana a wannan yanki. Paisley da sauran shugabannin ´yan protestant sun bayyana tayin wanzar da zaman lafiya da IRA ta yi da cewa ba sabon abu ba ne, domin a lokutan baya ma kungiyar ta sha daukar alkawura da dama amma ba ta cikawa. Saboda haka dole ne a gani a kasa musamman wajen kwance damarun mayakan ta kana kuma dole ne IRA din ta yi watsi da ayyuka irin na ´yan daba, kamar kisan babu gaira da fashi da makami da fataucin miyagun kwayoyi da kuma hukunta wadanda suka juya mata baya.

Wadannan ayyukan ne kuwa suka jawowa IRA din koma baya a arewacin Ireland, sannan ta rasa dukkan taimako da goyo baya da ta ke samu a cikin gida da kuma waje. Shi ya sa yanzu hanya daya tilo da ta rage mata ita ce ta neman wanzar da zaman lafiya. Saboda haka ake ganin da kanshin gaskiya tayin zaman lafiyar da shugabannin kungiyar ta IRA suka yi to sai dai yaya batun biyayya ga shugabanni a cikin kungiyar kan ta?

A nan dai akwai tambayoyi da dama da ke bukatar amsa. Wai shin idan IRA zata yi amfani da hanyoyi siyasa wajen cimma manufofinta to mai zai faru da bangaren ta na siyasa wato Sinn Fein? Ya ya shugannin ta zasu kasance shin tsofaffin ´yan ta´adda za su yi mata jagora kuma ya jama´a zata karbe ta? Da farko dai dole a jira a ga yadda ´yan protestant zasu tinkari sabon yanayin da aka shiga, domin sun fi so Ireland Ta Arewa ta ci-gaba da zama karkashin Birtaniya. Yayin da IRA da kuma Sinn Fein ke son a hade lardin da janhuriyar Ireland. Ga yadda yanayin zaman lardin ya ke a yanzu dole Paisley da shugaban Sinn Fein Gerry Adams su kafa wata gwamnatin hadin guiwa don ba wa arewacin Ireland din damar komawa ga matsayin sa na mai cin gashin kai.

Ko da yake Paisley na adawa da haka saboda rushewar gwamnatin mulkin cin gashin kai ta farko a Ireland Ta Arewa sakamakon kin da IRA ta yi na ajiye makamanta, amma Paisley bai da wata hujjar yiwa wani sabon shirin kafa sabuwar gwamnatin karar tsaye, muddin IRA ta kwance damarun mayakanta. Dole ne kuwa ta hanzarta yin haka don ba wa ranar 28 ga watan yulin shekara ta 2005 damar shiga cikin tarihi inda zaman lafiya ya maye gurbin yaki kamar yadda Tony Blair ya yi fata.