1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halinda ake ciki a Somalia

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 2, 2007

Gwamnatin wucin gadi ta kasar Somalia ta kafa wuraren da mayakan kasar zasu mika makamansu cikin birnin Mogadishu na tsawon kwanaki uku,a kokarinta na maido da zaman lafiya cikin birnin.

https://p.dw.com/p/Btwp
Muhammad Ali Gedi
Muhammad Ali GediHoto: AP

Tun a ranar litinin ne firaminista Ali Muhammad Gedi yace dole ne yan Somalia su mika makamansu,ko kuma dakarunsa su kwace da karfin tuwo,bayan waadin na kwanaki uku.

Gedi ya kuma mika tayin ahuwa ga mayakan da suka mika makamansu,wadanda suka ki kuma zaa bisu duk inda suka shiga.

“dakarun gwamnati tare da hadin kan sojojin Habasha suna fatattakar yan tawaye kuma zsu ci gaba da yin hakan har sai baba ta gani”

Su dai mayakan islaman sun fice daga dukkan yankuna da suke rike da shi,rahotanni kuma sunce sun kama hanyarsu ta zuwa kasar Kenya.

Inda gwamnatin Somalia ta bukaci Kenyan data rufe bakin iyakokinta.

Kenyan ta sanarda rufe oyakokin nata tare da tsare wasu mayakan islaman.

Ali Gedi a nashi bangare yace sun kame yan tawaye na Habasha da mayakan larabawa a lokacinda suka fatattaki mayakan na islama daga kudancin kasar da suke rike da shi na tsawon watanni shida.

Tunda farko gwamnatin Somalia da mai bata goyon baya Habasha sunce mayakan kasashen ketare suna taimakawa magoya bayan kotunan islama.

Gwamnatin ta Somalia ta zargi musamman abokiyar gabarta Eritrea,tana mai cewa,ta aike da daruruwan sojojinta domin suyi yaki kafada da kafada da gamaiyar kungiyoyin islama na kasar.

Eritrea dai ta karyata wannan zargi,tana mai cewa Habasha ce tayi katin shaidar dan kasarta na bogi ta warwatsa su a cikin Somalia domin ta batawa Eritrea suna.

Ya zuwa yanzu dai Gedi yace dakarun Habasha zasu fice da zarar an samu zaman lafiya a Somalia.

A halinda ake ciki kuma,firaministan Habashan Meles Zenawi ya roki taimakon kudi kasashen duniya domin ci gaba da aikin da sojinsa suka fara a Somalia,yana mai cewa dakarun nasa zasu iya ficewa nan da makonni biyu.

Tun farko Meles Zenawi yayi watsi da kira da kasashen larabawa da na Afrika sukayi masa na gaggauta janye dakarunsa daga Somalia.

Sai dai kuma akwai alamun cewa kalaman Zenawi sun sabawa na takwaransa Gedi a makon daya gabata inda yace dakarun Habasha zasu kasance a Somalia har iya tsawon lokacinda suke so.

Haka shima ministan harkokin wajen Habasha Seyoum Mesfin yace ya kamata kasashen duniya su taimaka wajen daukar nauyin Somalia.(o-ton)

Yanzu haka dai shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni da wani babban jamiin diplomasiya na Amurka zasu tattauna yadda zaa raba daukar nauyin farfado da Somalia.

Shugaban kasar Kenya kuma Mwai Kibaki ya sanrda shirye shiryen kiran wani babban taro na yankin domin tattauna hanyoyin da zaa maido da zaman lafiya mai dorewa a Somalia.

Manazarta dai sunce dadewar Habasha a Somalia zai iya tunzura yan Somalia,wadanda suka taba yaki har sau biyu tsakaninsu da Habasha kan batun lardin Ogaden dake kudancin Habasha.

Sun kuma yi gargadin cewa samun galaba akan mayakan islaman ba shine zai kawo karshen garari da jamaar kasar Somalia miliyan 10 suka samu kansu a ciki ba.