1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halinda ake ciki yau talata a Iraki

Zainab A MohammadSeptember 13, 2005

Binciken yan tawaye daga gida zuwa gida a Tal Afar

https://p.dw.com/p/BvZi
Hoto: dpa

Wayewan gari yau talata,dakarun Amurka dana Iraki sun shiga sako sako,suna neman yan takife da suke zargi da boyewa a garin Tal Afar ,dake arewacin Iraki.

Dakarun hadin gwiwan dai naciga da bincike daga gida zuwa gida,da zummar cafke yan takifen ,wadanda a fadansu yanzu basu da wata kwanciyar hankali.

Commandan rundunar Amurka na uku dake jagorantar wannan ayarin,Conel H.B McMaster ,yace akasarin garin na tal afar a yanzu haka yana hannunsu.Yace tuni yan yakin sunkurun suka tsere daga inda suke kai hare hare,inda suka shiga boyewa a gidajen mazauna garin,wanda adalilin hakane dakarun ke shiga gidaje suna gudanar da bincike.

Kimanin dakarun Iraki dubu 6 dana Amurka dubu 4 nedai suka afkawa garin na Tal Afar ,wadanda kuma suka tsananta sumamen nasu a karshen makon daya gabata,bayan daukan kwanaki masu yawa suna dauki ba dadi dayan yakin sunkurun dake fake a wannan gari dake arewacin Iraki.

Major James Gallivan na rundunar Amurka dai yace akalla an kasha yan yakin sunkuru 150,ayayinda aka cafke kimanin 400.

To sai dai bias dukkan alamu akwai sabanin yawan yan yakin sunkuru dake zaune a wannan gari,domin a wani general na Amurka a kwanakin baya ya sanar dacewa akwai kimanin yan tawaye 350 zuwa 500 dake boye a garin na Tal Afar.To amma wani Lieutenant na kasar Iraki yace yana iya kasancewa rabin wadanda aka kiyasta din sun tsere daga Tal afar kafin a kai musu wannan hari.

Daga cikin wadanda aka cafke inji rahotanni daga yankin,akwai mayakan kasashen ketare guda 30,wadanda suka hadar day an Syria 20 da yan Afganistan da kuma yan Saudi Arabia.

Ayau tarlatan dai dakarun iraki wadanda suka hadar da mafiyawan yan darikar Shia sunyi ta cafke mutane suna mikasu wa dakarun Amurka domin cigaba dayi musu bincike.

A hannu guda kuma akalla yan Irakin 3 ne suka rasa rayukansu ,ayayinda wasu 12 suka samu raunuka a hare hare daban daban a kewayen kasar.

Wani farar hula ya rigamu gidan gaskiya,ayayinda wasu 11 suka samu raunuka lokacinda bomb ya tarwatse cikin wata mota kirar Bus dake dauke da pasinja.

A yayinda a fadar kasar wasu yan bindiga dadi suka bindige wani direban babbar mota da maitaimakinsa,ayayinda suke kokarin kai kayan yin rumfunan gudanar da zaben raba gardama dazai gudana a ranar 15 ga watan gobe dangane da kundun tsarin mulkin Irakin.Bugu da kari wani mutun guda ya jikkata a gunduwar dora dake kudancin kasar.

Kasazalika wasu rokoki 5 sun tarwatse a cikin birnin bagadaza.Biyu sun fada yankin Green zone dake dauke da manyan jamian gwamnati,kuma wanda keda ingantaccen tsaro da kariya,ayayinda guda biyu suka fada wani fili ba tare da raunana kowa ba.

To sai dai rahotanni daga harin bomb din mota da yammacin jiya a wajen wani wurin cin abinci ,yah aura zuwa biyar,ayayinda Karin mutane uku sukace ga garinku a daren jiyan sakamakon raunuka da suka samu.

A wata sabuwa kuma Syria tayi Allah wadan zargin da Amurka tayi mata,nacewa tana barin masu tsattsauran raayin addini ,shiga ta hanyoyin sata zuwa cikin Iraki.

A jiya litinin nedai Jakadan Amurka a Iraki Zalmay Khalilzad,ya gargadi Damascus ,adangane da zargin da gwamnatin Amurkan keyiwa ,magabatan Syria na tallafawa yan yakin sunkuru suna kwarara cikin Iraki.