1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas da Fatah sun ƙudurci girka gwamnatin riƙwan ƙwarya

September 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bujp

Ƙungiyoyin Fatah da na Hamas na ci gaba da tantanawa a yunƙurin girka, gwamnatin haɗin kasa a Palestinu, da ta ƙunshi ɓangarorin 2.

Babban burin wannan gwamnati shine na samar da haɗin kai bayan rigingimun da su ka ɓarke tsakanninmagoya bayan hamsa da na Fatah a kwanakin baya.

Kazalika, su na masu buƙatar cimma nasara, cire takunkumi da ƙasashen turai da Amurika, su ka sakawa Palestinawa, tun watan Janairu da ya gabata, a sakamakon rinjaye, da Hamas ta samu, a Majalisar Dokoki.

A nasa ɓangare, tunni, shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas, ya alƙawartawa ma´aikatan gwamnati, biyan bassukan albashin watani 6, da su ka tambayo, bayan girka sabuwar gwamnatin.

Ƙungiyar gamayya turai, a cikin sanarwar da ta hiddo, ta yi lalle marhabin, da shawara da Palestniawa su ka yanke, ta girka gwamnatin haɗin kan ƙasar.

Itama Isra´ila, ta bada sanarwar belin wasu daga yan majalisun dokoki, da ministocin Hamas da ta kame, a yunƙurin ceton sojan ta ɗaya, da a ke ci gaba da garkuwa da shi, a zirin gaza.