1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas - Gabas Ta Tsakiya

January 31, 2006

Rukunin nan na bangarori hudu, wanda ya kunshi Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Hadin Kan Turai da kasashen Amirka da Rasha, ya gabatad da sharuddansa na ci gaba da damawa da Hukumar Falasdinawa, wadda Kungiyar Hamas za ta jagoranci, bayan lashe zaben Falasdinawan da ta yi a makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/Bu1y
Khaled Mashaal, shugaban Kungiyar Hamas.
Khaled Mashaal, shugaban Kungiyar Hamas.Hoto: AP

Bukatun da rukunin Gabas Ta Tsakiya ya gabatar wa sabbin mahukuntan Falasdinawa, musamman ma dai kungiyar na ta Hamas, wato an tsara su ne dalla-dalla. Rukunin dai, ya kunshi Kungiyar Hadin Kan Turai ne da Majalisar Dinkin Duniya, da Rasha da kuma Amirka, wadanda su ne ke mara wa shirin nan na daftarin samad da zaman lafiya a yankin na Gabas Ta Tsakiya baya. Da yake gabatad da bukatun a wani taron maneman labarai jiya a birnin London, babban sakataren Majalisar dinkin Duniya Kofi Annan, ya bayyana cewa:-

„Bisa ra’ayin da rukunin ya amince da shi dai, dole ne duk mambobin sabuwar Hukumar Falasdinu da za a kafa su dau alkawarin kaucewa daga duk wasu tashe-tashen hankulla, su amince da wanzuwar Isra’ila tamkar kasa su kuma kiyaye duk ka’idojin da aka riga aka yarje a kansu, wato har da kundin nan na daftarin samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.“

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, Kofi Annan, a madadin rukunin, ya sake nanata wasu kalmomin da tuni shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel ta yi amfani da su a cikin jawaban da ta yi yayin ziyararta a Gabas Ta Tsakiya, da kuma wadanda shugaba Bush na Amirka da sakatariyar harkokin wajensa Condoleeza Rice su ma suka yi amfani da su a cikin bayanan da suka game da kungiyar ta Hamas. Ita dai Condoleeza Rice, a cikin bayananta cewa ta yi:-

„Zaßaßßaun wakilan Falasdinawa na da alhakin ganin cewa, fatar da al’umman Falasdinun ke yi, na samun kyakyawan hali na rayuwa da zaman lafiya ya tabbata. Ba za a iya kuwa cim ma wannan zaman lafiyar ba, sai ta hanyar warware rikicin Gabas Ta Tsakiyan cikin ruwan sanyi, da kuma amincewa da wanzuwar Isra’ila tamkar kasa.“

Kofi Annan dai ya bayyana cewa, nan gaba, za a jißinta duk wani taimakon da za a bai wa Falasdinawan ne da kiyaye ka’idodjin wadannan sharuddan. Kasafin kudin Hukumar Falasdinawan dai ya kai dola biliyan daya da digo 5. Fiye da rabin wannan kudin dai na zuwa ne daga Amirka da kuma kungiyar Hadin Kan Turai.

Babban jami’in Kungiyar Hadin Kan Turan, mai kula da batutuwan harkokin ketare, Javier Solana, wanda shi ma ya halarci taron na birnin London, ya bayyana cewa:-

„A shirye kungiyar EUn take, ta ci gaba da ba da gudummowa ga inganta fannin tattalin arzikin Falasdinawan da kuma kafa musu kasa ta dimukradiyya. Amma dole ne su kiyaye duk wadannan ka’idojin.“

Wadannan bayanan da rukunin Gabas Ta Tsakiyan ya tsara su a hankali dai, na nufin bai wa `yan kungiyar ta Hamas wata dama ne yadda za a dama da su. Kiran da aka yi musu na kaucewa daga duk wasu tashe-tashen hankulla dai, ba daidai yake da juya wa yin mafani da makamai baya ba. Bugu da kari kuma, duk da cewa rukunin na neman kungiyar Hamas din ta amince da wanzuwar Isra’ila tamkar kasa, amma hakan ba wani sharadi ba ne, wanda sai ta cika shi kafin a dama da ita. A kalla dai, a halin da ake ciki yanzu, rukunin ba ta tsai wa kungiyar wani wa’adi ba.

A takaice dai za a iya cewa, gamayyar kasa da kasa na son ta bai wa kungiyar Hamas din wani lokaci ne na yin tunani, tare da fatar cewa, nan ba da dadewa ba, za ta bayyana shirinta na tafiyad da siyasa ta hannunka mai sanda.