1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ka iya kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra´ila

January 29, 2006
https://p.dw.com/p/BvAQ

Shugaban Hamas Mahmud Zahar ya ce kungiyar sa ta ´yan kishin Islama ba zata amince da wanzuwar Isra´ila amma a tana iya kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ita. A cikin wata hira da jaridar Sunday Telegraph ta Birtaniya Zahar yayi kira ga kasashen duniya da su amince da Hamas a matsayin sabuwar halattaciyar gwamnatin Falasdinawa. Kungiyar wadda ta lashe zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinawa a ranar laraba ta ki ta ajiye makamanta. An dai shiga wani mummunan yanayin siyasa a yankunan Falasdinawa sakamakon wannan nasara ta Hamas, inda a jiya dubban magoya bayan kungiyar fatah suka gudanar da zanga-zanga a yankunan Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza. A Ramallah wasu ´yan bindiga na kungiyar Fatah sun hau kan rufin ginin majalisaar dokoki inda suka yi ta harbi cikin iska. Sojojin sa kai na Fatah tare da ´yan sanda sun kwace ginin majalisar dokoki dake Zirin Gaza.