1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas na da ´yancin bijirewa mamayar Isra´ila-inji Mashaal

January 28, 2006
https://p.dw.com/p/BvAU

A wani labarin kuma shugaban bangaren siyasa na Hamas Khalid Mashaal ya ce kungiyarsa na son kulla kawance da sauran kungiyoyin Falasdinawa saboda haka yayi kira ga kasashen duniya da su girmama nasarar da kungiyar ta samu a zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinu. A lokacin da yake magana a Damaskus babban birnin Syria Mashaal ya ce burin su shine yiwa Hukumar Falasdinu kwaskwarima, ci-gaba da bijirewa Isra´ila sai kuma abin da ya kira daidaita sahu a cikin gida. Mashaal ya ce gwagwarmayar wani ´yancinsu ne matukar yankunan su na karkashin mamayar Isra´ila. Mashaal ya ce ba ya jin za´a sabunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra´ila wadda Hamas ta janye daga ita a karshen shekarar da ta wuce. A kuma halin da ake ciki baradan Al-Aqsa na bangaren kungiyar Fatah ta ba da sanarwar janye daga yarjejeniyar dakatar da yaki da Isra´ila bayan da fatah ta sha kashi a zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinu. Al-Aqsa ta ce yanzu zata auna harsasanta akan Isra´ila da kuma shugabannin Fatah masu cin hanci da rashawa.