1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta lashi takobin daukar fansa bayan wani farmakin Isra´ila

February 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9K

Bayan farmaki ta sama da Isra´ila ta kai a Birnin Gaza, wanda ya halaka Falasdinawa 3, kungiyar Hamas ta ba da sanarwar daukar fansa. Shugaban Hamas Khalid Mashal ya ce kungiyarsa na da ´yancin kare kanta daga duk wani hari na Isra´ila. Wannan harin dai shi ne irinsa na farko da Isra´ila ta kai tun bayan nasarar da Hamas ta samu a zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinawa da aka gudanar a ranar 25 ga watan janeru. Hamas dai na shan matsin lamba daga kasashen duniya na ta daina kaiwa Isra´ila hare hare. A wani labarin kuma wata Bayahudiya a garin Petah Tikvaf ta rasu bayan da wani Bafalasdine ya daba mata wuka. ´Yan Isra´ila 5 sun samu rauni a wannan hari wanda aka ce yana da alaka da siyasa. A wata sabuwa kuma Isra´ila ta amince ta turawa hukumar mulkin Falasdinawa miliyoyin dalar Amirka na kudaden kwasta bayan ta dakatar da yin haka sakamakon lashe zaben da Hamas ta yi.