1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta maida martani ga Turai da Amurika

January 31, 2006
https://p.dw.com/p/BvA6

Kasashen Amurika da na Turai na ci gaba da matsa kaimi ga kungiyar da ta yi watsi da akidodjin ta na kai hare hare ga Israela da kuma amincewa da hallata kasar ta Israela.

Wannan kiranye kiranye sun biwo bayan gagaramar nasara da kungiyar ta Hamas, ta samu a zaben yan majalisun dokokin kasar Palestinu a makon da ya gabata.

A taron hadin gwiwa da su ka shirya ranar jiya litinin, kungiyar gamaya turai, Rasha, Majalisar Dinkin Dunia da Amurika,Turai da Amurika, sun tabatar da cewa watsi da wannan manufofi su ne sharradin da zai sa, su bada taimako ga sabuwar hukumar Palestinu.

A yayin da ya ke maida martani ga wannan kalamomi, shugaban kungiyar Hamas, Khaled Mechaal, ya sannar cewa ko da mafarki, Kungiyar Hamas ba za ta taba kauce wa daga aniyar ta ba, ta haramta Isra´ila muddun hukumomin wannan kasa za su ci gaba da ci da gumin Palestinawa.

Maganar tallafi kuwa, Hamas ba ta bukata, in har sai ta cika wannan sharadi.

Shugaban Hamas ya yi tunni ga wannan kasashe cewar, Palestinawa su ka zabi Hamas ta hanyar kuiri´a, a gamne da haka bat a kamata ba su kafa masu klaran tsana don biyan burin yahudawa.