1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta nada majalisar ministoci

March 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4l

Kungiyar kishin Islama ta Hamas ta kammala tsara sunayen majalisar ministoci wanda ta ke fatan amincewar Shugaba Mahmoud Abbas. Sabon P/M yankin, Ismaila Haniya ya ce zai mika sunayen ga Mahmoud Abbas a ranar Lahadi. Ismaila Haniya ya shaidawa taron manema labarai cewa babu kokwanto za su cimma nasarar aiwatar da alhakin da jamaá suka dora musu. Rahotanni sun baiyana cewa manyan amintatun a kungiyar Hamas su ne aka nada a muhimman mukamai. Majiyoyi sun baiyana cewa an nada Abdel-Razeq, farfesa a fannin tattalin arziki, a matsayin ministan kudi yayin da Mahmoud al-Zahar zai rike mukamin ministan harkokin waje, sai Saeed Seyam wanda aka nada a mukamin ministan alámuran cikin gida. Wata majiya ta kusa da shugaban Palasdinawan Mahmoud Abbas ta baiyana cewa ko da yake ba shi da niyar kin amincewa da sunayen ministocin amma zai bukaci Hamas ta yi wasu yan gyare gyare a jadawalin sunayen. Jamíyar Fatah ta Mahmoud Abbas da sauran kananan jamíyu na fuskantar matsin lamba daga Amurka ka da su shiga gwamnatin hadin kan kasa da jamíyar Hamas ke shirin kafawa.