Hamas ta nemi a fita intifada ranar Juma′a | Labarai | DW | 07.12.2017

Labarai

Hamas ta nemi a fita intifada ranar Juma'a

An dai shiga fargaba tun bayan da Trump ya ce Birnin Kudus ya zama babban birnin Isra'ila yayin da Falasdinawa suka ce babban birninsu ne.

Gaza - PK von Hamas-Chef Ismail Haniyeh wegen Jerusalem-Status (Reuters/M. Salem)

An dai shiga zanga-zanga a yankin Falasdinawa bayan da Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila. Shugaban kasar Turkiya Tayyip Erdogan da Fafaroma Francis sun amince a wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan rana ta Alhamis cewa duk wani kokari na sauya matsayar Birnin Kudus abu ne da ya kamata a kauce masa kamar yadda ofishin Erdogan ya bayyana.

A cewar majiyar labarin dukkanin shugabannin biyu Erdogan da Fafaroma sun amince cewa birnin Kudus waje na ibada mai tsarki ne da mabiyan addinin Musulinci da Kirista da ma mabiya na addinin Yahudu. Tuni dai kungiyar Hamas ta sha alwashi na fita intifada a karo na uku a ranar Juma'a abin da ke haifar da fargabar kwarara ta jini da rasa rayuka. 

 

Albanian Shqip

Amharic አማርኛ

Arabic العربية

Bengali বাংলা

Bosnian B/H/S

Bulgarian Български

Chinese (Simplified) 简

Chinese (Traditional) 繁

Croatian Hrvatski

Dari دری

English English

French Français

German Deutsch

Greek Ελληνικά

Hausa Hausa

Hindi हिन्दी

Indonesian Bahasa Indonesia

Kiswahili Kiswahili

Macedonian Македонски

Pashto پښتو

Persian فارسی

Polish Polski

Portuguese Português para África

Portuguese Português do Brasil

Romanian Română

Russian Русский

Serbian Српски/Srpski

Spanish Español

Turkish Türkçe

Ukrainian Українська

Urdu اردو