1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta zabi Isma´il Haniyeh a matsayin saban Pramistan Palestinu

February 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7l

Kungiyar Hamas da ta lashe zaben yan majalisun dokokin Palestinu a watan Janairu da ya wuce ta zabi Isma´il Haniyeh a matsayin saban Praminista.

Zabbabun yan majalisu dokoki kasar ne su ka yanke wannan shawara wani zama taro da su ka yi ranar jiya alhamis a Rammallah.

Ranar asabar mai zuwa za su gabatar da sunan saban Praministan ga shugaban kasa Mahamud Abbas.

Zaben Isma´il Haniyeh a matsayin Praministan Hamas, bai baiwa masharahanta a yankin mamaki ba, kasancewar sa, daya daga na hannun damar tsofan shugaban kungiyar Scheik Yacine Ahmed da rundunar Israela ta kashe a shekara ta 2004.